Kannywood
Bidiyo : Saratu Daso Tayi Martani Mai Zafi Ga masu Aibanta Halittar Matar Sahabi Na kwana casain
Wannan wani sabon bidiyo ne da jaruma kuma uwa a masana’antar kannywood wanda tayi bidiyon ne ga al’ummar duniya akan Ali hussaini wanda anka fi sani da sahabi madugu a cikin shirin Kwana Casain da tashar arewa24tv ke haskakawa duk sati.
Saratu daso tace munyi murna da Allah ya bashi damar yayi aure amma wasu suna kushewa wai ba kyakkyawa bace ita ba ce, bata dace da shi ba.
Wanda saratu daso tayi matukar jin zafi sosai wanda ta nuna cewa shin so kuke yaje ya kama bariki da yan mata na banza?.
Shin daman ba so da kauna ke sanya ayi aure ba ko hali sai dole ya nema fara kyakkyawa babu hali a gareta ba.?
Duk amsar Wannan maganganu suna cikin faifan wannan bidiyo sai ku kalla kuji.