Shugabancin Buhari: Ran Akuya Ya Fi Na Dan Arewa Daraja – Zaharadeen sani
Jarumin Finafinan Hausan ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan Bidiyo da ya sanya a shafin shi na Instagram domin nuna damuwa da takaici akan halin da jihar Zamfara da yankin Arewa yake ciki na tabarbarewar tsaro.
Zaharadeen Sani ya kara da cewar an wayi gari a kullum ana satar mutane kamar Kaji a yankin arewa, a yau ‘yan ta’addan sun gagari Zamfara, sannan jama’a suna ji suna gani zuwa Abuja ta Mota ya gagare su daga Kaduna sai dai abi jirgin kasa, kuma abin takaici da haushi babu wani abu da gwamnati tayi akan magance matsalar.
Kwararren dan wasan Hausan ya nuna damuwa matuka da yadda babu dama a fadi gaskiya akan gazawar Buhari akan tsaro, da mutum ya yi magana sai a ce ai shi dan PDP ne, alhali yankin kudanci suna cikin walwala da jin dadi, idan ka ji wata matsala a kasar nan to a Arewa ne, yau an wayi gari ran Akuya ya fi na dan Arewa daraja a kasar nan.