Kannywood
Yanzu Yanzu : Adam A Zango Yabar Buhari Ya Koma Tafiyar Atiku
Advertisment
Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya shirya tsaf don ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP. Kamar yadda majiyarmu ta samo rahoton.
Rahoton na bayyana cewa, Adam Zango ya tattauna da na hannun daman dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da wasu shugabannin PDP a jiya Laraba a Abuja.
Rahoton ya kara da cewa, a tattaunawar shugabannin PDP suka yi da jarumin sun yi kokarin gamsar da shi akan ya canza jam’iyya daga APC zuwa PDP.
Da farawa da iyawa an baiwa adam a zango ambassador na pdp
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com







Ai dama Adam A Zango ba yau ya saba yin abun kunya ba. KWADAYAYYE