Addini

Kungiyar Tijjaniya tayi karin haske a kan goyon bayan takarar Buhari – Sheikh Ibrahim Maqari

Jigo a darikar Tijaniyyah na Najeriya, Sheikh Ibrahim Maqari ya nesanta kungiyar daga goyon bayan tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zabe na ranar 6 ga watan Fabrairu.

A ranar Lahadi ne wata kungiya mai suna “Tijjaniya SUFI Movement of Nigeria” ta yi kira ga magoya bayanta a dukkan sassan Najeriya su zabi Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.

A sanarwar da kungiyar ta fitar da hannun shugabanta, Timasaniyu Ahmed-Rufai, kungiyar ta ce ta cimma matsayar goyon bayan Buhari ne karo na biyu saboda “an gwada shi kuma an gamsu da nagartarsa”.

Sai dai babban shehin dariqar Sheikh Maqari wanda shine babban limamin a Masallaci na Abuja ya nesanta kungiyar ta Tijaniyya daga wannan goyon bayan inda ya ce dukkan ‘yan kungiyar su zabi duk wanda suke so bisa abinda zuciyarsu ta gamsu da shi.

Yace “Tijanniyah tsari ne na sufanci ba kungiya ba. Tijaniyah ba ta tilastawa mabiyanta zaban wani dan takara ba,” inji Maqari.

“Abinda shugabanin Tijyaniyah suka ce shine mabiyansu su zabi shugabanni masu gaskiya da rikon amana, halaye na gari da kishin kasa ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasar da suke ciki ba.
” Don kuwa Kowa zai Kare kansa dangane da zabin da ya yi a gaban Allah (SWT) a gobe kiyama. “

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button