[Bidiyo] Malam zan Iya baiwa Mahaifina zakkat? – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Tambaya
Assalamu alaikum warahamatullah malam ina da tambaya nayi noma zan fitar da zakkat ya hallata na baiwa mahaifina/babana da ƙanena?
Amsa
Ƙanen ka dai idan kayi haka ae ka wulakanta babanka ace masu Layin karba zakka harda babanka a ciki,haba akarmukallahu 10% ne fah za’a bawa da zakkar nan to 90% fah.
Malam ya kara da cewa idan ka sanya babanka a cikin 10%,90% din kuma waye zan ci ,ae darajar babanka ya kamata ya shiga cikin wancan 90% din?.
Wancan 10% din abaiwa masu ban tausayi zakkat nan ba mahaifinka ba, kada ma ka kuskura ka saye yin wannan tambaya ka baiwa babanka zakkat darajarsa tafi haka.
Ga cikakken bayyani a cikin faifan bidiyo da tashar YouTube mai Suna Daurawa Tv na wallafa.
https://youtu.be/dsAZ39EYqlI