Ta’addancin Da Ake A Nigeria Kwangila (karanta)
Cibiyar nazari da bincike akan al’amuran duniya wato “Centre For Global Research” ta tabbatar da cewa hukumar leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaro na ‘kasar Amurka “Central Intelligence Agency” (CIA) tana da hannu wajen tsara ayyukan kungiyar Boko Haram a Nigeria
Akwai dalilai da yasa CIA take tallafawa ayyukan ta’addanci a gabas ta tsakiya da kuma nahiyar afirka, kafin kaji haushin Datti Assalafiy don yace ta’addancin Boko Haram kwangila ne duk wanda yake da bukatar karanta cikekken bayanin wanda cibiyar nazari da binciken al’amura na duniya ta fitar a shafinta na website ga link din kamar haka: https://www.globalresearch.ca/is-boko-haram-a-cia-covert-op-to-divide-and-conquer-africa/5431177
Yana da kyau mu fahimci cewa Amurka ita ta kirkiri kungiyar ISIS lokacin Barak Obama, hatta shugaban ‘kasar Amurka na yanzu Donald Trump ya tabbatar da wannan kai tsaye ya zargi Obama da hannu wajen kafa kungiyar ISIS, amma shima da ya zama shugaban ‘kasa giyar mulki ta bugashi munga yayi shiru akan ISIS, gashi yau ISIS ita ke taimakon kungiyar Boko Haram kai tsaye
Misali cikin sauki da za’a fahimci yadda Amurka ta tallafawa ayyukan ta’addanci a nahiyar afirka shine yadda ta dauki kwangilar ‘yan tawayen ‘kasar Libya suka yiwa tsohon shugaban ‘kasar Kanar Muhammad Ghaddafi bore, Amurka ta jibge manyan makaman yaki a Libya, ta gayyato taron dangin rundinar tsaron hadin gwiwa na kasashen turawa (NATO) sukazo suka yaki Ghaddafi, bayan an kasheshi suka bar makaman ya fada hannun ‘yan tawayen da yau sune suka rikide suka zama ‘yan ISIS, hatta makaman da ‘yan bindigar da suka addabi jihar Zamfara suke amfani dashi duk daga Libya suke samu, haka ma Boko Haram, yau Lbiya ta zama cibiyar assasa ayyukan ta’addanci a duk fadin nahiyar afirka
Kuma shi wannan shugaban ISIS din wato Abubakar Albaghdadi tsohon jami’in leken asiri ne na Amurka wato CIA, nayi rubutu akan wannan shekaru biyu da suka gabata, sannan yayi aiki da hukumar leken asiri na ‘kasar Isra’ila wato MOSSAD kamar dai yadda tsohon shugaban kungiyar Al-qa’idah Osama bin Laden yayi aiki da hukumar leken asirin Amurka (CIA) daga karshe sukayi amfani dashi wajen cimma ajandarsu a kasashen Larabawa
Muma nan Nigeria daya daga cikin mutanen da sukaci kudin makamai jami’in leken asirin Amurka ne (CIA) idan baku sani ba, wato jama’a ku fahimci cewa haka kawai gwamnatin Buhari ba zata cigaba da tsareshi a gidan yari ba duk da hukuncin kotu na a bada belinsa, wanda basu sani ba su sani; hatta lokacin da su Obasanjo sukayi yunkurin kifar da gwamnatin Janar Sani Abatcha basuci nasara ba, wannan mutumi da gwamnatin Buhari take tsare dashi yana daga cikin wanda suka kimtsa ham6arar da gwamnatin Sani Abatcha a wancan lokacin, amma ya sulale ya gudu Amurka ta bashi mafaka saboda jami’in leken asirinta ne.
Bai dawo wannan ‘kasar ba har sai da Sani Abatcha ya mutu
Kuma jama’a ku duba kuga makirci irin na tsohon shugaban ‘kasa Goodluck Jonathan, lokacin da ‘yan kwangilar ta’addancin Boko Haram suka kifar da tsohon mai taimakawa shugaban ‘kasa da shawara akan tsaro Janar Andrew Azazi a cikin jirgi ya hallaka saboda yace sune Boko Haram kawai sai ya maye gurbinsa da wannan jami’in leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaro na Amurka, suka kasafta kudin makamai sukayi abinda sukaga dama wajen karfafa Boko Haram
Mu dage sosai da addu’ah ‘yan uwa musulmi, ta’addancin Boko Haram tallafin da kungiyar take samu ya wuce tunanin duk wani mai tunani, ya ishe mu babban musali yadda rundinar sojin Nigeria ta kama kungiyoyin kare hakkin bil’adama na duniya mallakin turawa da hannu dumu dumu suna taimakon Boko Haram rundinar soji ta dakatar dasu, amma dakatarwan bai kai awanni 24 ba aka zafafa kira ga rundinar sojin Nigeria dole ta janye dakatarwan saboda suma abin yafi karfinsu
Don haka mu munyi imani da Allah babu wanda yafi karfin Allah (SWT) mu mayar da al’amarin mu ga Allah mu rokeShi.
Yaa Allah muna rokonKa ka rusa duk wanda suke da hannu wajen tallafawa kungiyar Boko Haram ta kowace hanya