Ya Tabbata Nigeria Tana Yaki Da Kungiyar ISIS Na Duniya Ne Kuma Me Yasa Boko Haram Suka Zafafa Hari?
Ina so kowa ya karanta wannan rubutun a tsanake don fahimtar asalin abinda yake faruwa game da yaki da ayyukan ta’addanci a halin yanzu
Kungiyar da take saka ido akan ayyukan ta’addanci na duniya karkashin majalisar dinkin duniya, wato “International Terror Monitoring Group” (ITMG), ta fitar da rahoto tace; wadanda a yanzu suke daukar nauyin kungiyar Boko Haram kai tsaye itace kungiyar ISIS na duniya karkashin jagorancin Muhammad Abubakar Albaghdadi, ISIS ita ke taimakon Boko Haram ta reshenta na “Islamic States West African Province” (ISWAP) karkashin jagorancin ‘dan gidan Muhammad Yusuf na biyu wato Habib Muhammad Yusuf (Abu Mus’ab Al-barnawiy)
Hukumar kula da ayyukan ta’addanci na duniya (ITMG) a rahoton tace kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP reshen ISIS tana kokarin canza komai na tsarin ayyukan kungiyar Jama’atu Ahlussunnah Lidda’awati wal jihaad (JASLWID) wanda akafi sani Boko Haram bisa jarjejeniyar mubayi’ah da sukayi da ISIS na duniya sakamakon barazanar da ISIS ta yiwa kungiyar Boko Haram cewa zata janye daga bata dukkan tallafi saboda kasa cika yarjejeniyar da Boko Haram tayi da ita ISIS din
Yarjejeniyar ya shafi cewa dole Boko Haram su kwace ikon arewa maso gabashin Nigeria gaba daya su kafa sabuwar ‘kasar musulunci, kuma shekara uku ISIS ta dibar wa Boko Haram, sai dai gashi shekaru uku na yin yarjejeniyar ya kare Boko Haram bata cika ka’idar yarjejeniyar da sukayi da ISIS ba
(Jama’a idan ba’a manta ba shekaru uku kenan wato a shekarar 2015 Abubakar Shekau da su Abu Mus’ab Al-barnawiy suka yiwa kungiyar ISIS mubayi’ah lokacin suna tare, amma saboda wasu kura-kurai da aka samu a tattare da Shekau sai ISIS ta shugabantar da Habib Muhammad Yusuf Abu Mus’ab Albarnawiy a matsayin shugaba, wanda hakan ya haifar da rabuwa a tsakaninsu)
A rahoton hukumar kula da ayyukan ta’addanci na duniyar sunce kungiyar ISIS tana ganin kungiyar Boko Haram a matsayin wacce ta tabka asara na rashin wasu garuruwa da ta kama daga gwamnatin Nigeria a baya, don haka sai ISIS ta gargadi Boko Haram cewa zata raba hannun riga da ita saboda nasaran da rundinar sojin Nigeria suke samu akan Boko Haram musamman kwace babban sansanin Boko Haram na “sabilul-huda” da sojojin Nigeria sukayi a cikin jejin Sambisa, da kama wasu manyan mashiga da rundinar sojin Nigeria take da iko a yankin tabkin Chadi
Kuma idan har kungiyar Boko Haram ta kuskura ta rasa goyon baya daga kungiyar ISIS wannan yana nuni da kawo karshen kungiyar Boko Haram daga doron duniya, kuma babban burin kungiyar Boko Haram shine ya kasance sun cigaba da samun tallafin kwararrun mayaka da kayan yaki da harsashin bindiga daga kungiyar ISIS, saboda haka idan har ya kasance Boko Haram bata cika alkawarin yarjejeniya dake tsakaninta da ISIS ba to dukkan tallafi da take samu daga gareta zai tsaya, kuma zaiyi sanadin da sojojin Nigeria zasu share ruhinsu daga doron dubiya
Don haka abinda ake gani yana faruwa kungiyar Boko Haram suna ta zafafa hare-hare a arewa maso gabashin Nigeria kokari suke su karbi wasu yankuna domin su cika alkawarin yarjejeniya da sukayi tsakaninsu da kungiyar ISIS, imba haka ba to kungiyar ISIS zata raba hannun riga dasu, hukumar ITMG ta kara da cewa hatta harin da Boko Haram suke yawan kaddamarwa akan sansanin sojojin Nigeria kokari suke su nunawa ISIS cewa sun kwace ikon wasu garuruwa a arewa maso gabas, amma duk da wannan yunkuri na Boko Haram sun kasa cimma abinda suke so domin sojoji na fatattakarsu sosai
ITMG taci gaba da cewa; a yanzu da babban zabe ya kusa a Nigeria kungiyar ISIS ta zafafa kira ga Boko Hatam ta dage wajen ganin ta kwace ikon manyan garuruwa, ISIS tana wannan kiran ga Boko Haram tun watanni shida da suka gabata don ganin ba’ayi zabe ba a wasu sassan Nigeria, wanda hakan ka iya zamowa dalilin da zaisa a fasa yin zabe gaba daya a tarayyar Nigeria, wannan muradine kai tsaye daga kungiyar ISIS
Amma a halin yanzu dukkan alama ya nuna cewa da kamar wahala Boko Haram ta iya cikawa kungiyar ISIS burinta, saboda a halin da ake ciki yanzu Boko Haram bata da wani kwakkwaran shaida da zai nuna cewa tana rike da wata karamar hukuma daya a dukkan fadin jihohin arewa maso gabashin Nigeria, ba kamar yadda ya kasance a shekarun baya da sai da Boko Haram ta karbi ikon kananun hukumomi guda 16 a jihohin arewa maso gabas din Nigeria ba
Jama’a kunji bayani daga hukumar da take saka ido akan ayyukan ta’addanci na duniya, tun da jimawa mun fada muku cewa an karya kashin gadon bayan Boko Haram na Shekau, yanzu da kungiyar ISIS na duniya gwamnatin Buhari take yaki, abinda ya ragewa Shekau da za’ace yana da ‘dan karfi a kai shine harin kunar bakin wake, shi din ma yanzu an dauki lokaci bomb bai tashi ba a Nigeria, Alhamdulillah
Tsakani da Allah sojojin Nigeria suna iya bakin kokarinsu, kuma suna samun nasara akan ‘yan ta’adda, yanzu barazanar ISIS da ta kawo tallafi wa ISWAP ake fuskanta wacce take da babban sansaninta a yankin tabkin chadi, idan kun lura duk hare-haren da yake faruwa daga yankin tabkin chadi ne, zaiyi wahala kaji anyi hari ace harin ya fito daga inda Shekau yake da iko saboda an karyashi
Kuma abinda yake baiwa ISIS ‘dan nasara shine sunzo da sabon salo na yaki, domin manyan kwamandojin yakinsu ‘yan asalin ‘kasar Chadi ne kuma tsoffin sojojin ‘kasar Chadi da sukayi tawaye, sunfi kwarewa a yakin sahara (desert operations) yayin da sojojin Nigeria sunfi kwarewa a yakin sunkuru (bush operations), sannan wadannan ‘yan ta’addan ISWAP sunzo da sabon salo na dabarun yaki wanda yake basu nasara shine basa taba wanda duk ba jami’in tsaro ba, hakan zaisa al’ummar yankin ba zasu bada bayanan sirri ga dakarun sojin Nigeria ba
Don Allah kowa ya fahimci wannan, kada kowa ya amince ‘yan jari hujja da ‘yan shi’ah su rudar masa da tunani akan wannan yaki da ayyukan ta’addanci a arewa maso gabas, wallahi yadda a yanzu ISIS ta kawo tallafinta ga Boko Haram inda ace a gwamnatin PDP ne to ba karamar hukuma ba har jiha sukutum sai gwamnatin PDP ta damkawa Boko Haram domin ajandarsu ce wannan
Allah Mungode maKa
Allah Ka taimaki dakarun tsaron Nigeria Ka basu nasara akan dukkan wani nau’i na kungiyar ta’addanci a ‘kasarmu Nigeria Amin