Labarai

Na Tabbata Da Umaru Musa Yar’adua Na Da Rai Da Jam’iyyar APC Zai Yi Saboda Adalcinta, Cewar Hajia Bilkisu Kaikai

… PDP Ce Ta Jefa Kasar Nan Cikin Halin Tabarbarewar Tsaro Tun Farko
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Tsohuwar Mai ba tsohan Gwamna Ibrahim Shehu Shema shawara akan ilmin ‘yaya mata, wadda ta dawo jamiyyar APC Hajiya Bilkisu Kaikai, ta bayyana cewa sakamakon irin ayyukan alherai da Kuma gina kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Gwamna Masari ke Yi a jihar Katsina. Ta ce da Allah yasa Marigayi tsohan shugaban kasa malam Umaru Musa Yar’adua yana da rai da yanzu yana cikin jamiyyar APC.
Hajiya Bilkisu Kaikai ta bayyana haka ne a Karamar Hukumar Kusada a wajen taron gangamin yakin neman zaben Gwamna Aminu Bello Masari da yake yi a shiyyar Daura.
Bilkisu Kaikai ta cigaba da cewa duk wannan matsaloli na rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta, Jamiyyar PDPce ta asassa shi da gangan. Yanzu Kuma shugaba Buhari da Gwamna Masari suna yin bakin kokarin su domin kawo karshen fitinu, don hakamu mu ma al’umma my cigaba da yin addua samun dawamamme zaman lafiya a kasar nan.
Hajia Bilkisu Kaikai ta kara da cewa kowa ya san gidansu malam Umaru Musa Yar’adua nan to ga kanin shi uwa daya, uba daya Audu Soja to ga shi acikin wannan tafiya ta APC, don haka PDP ta mutu murus a jihar Katsina, da kasa baki daya. A PDP da na yi a baya yaye aka kaini Kuma yanzu na gyagyije Kuma na dawo APC cikin ‘yan uwana.
Daga karshe ta yi kira ga Mata da su jinkirta yin kunshi, har zuwa bayan zabe saboda idan mace na da kunshi naurar masu tantance masu zabe ba za ta tantance su ba. Don haka mu fito mu zabi Buhari da Gwamna Masari da sauran Yan takarar APC. An yi addua ga Marigayi tsohan shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua da sauran musulmi da suka Riga mu gidan gaskiya wadda shugaban jamiyyar ya Gabatar.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button