A fim ne na Musulunta ba A zahiri ba – Jim Iyke
Ban koma addinin Musulunci ba, in ji Jim Iyke
Jarumin masana’antar finafinai ta Nollywood, Jim Iyke, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ya musulunta.
A yau ne a ka wayo gari da rahotanni, har da hotuna da su ke nuni da cewa Iyke ya musulunta
Sai dai kuma a wani martani da ya yi, jarumin ya ƙaryata wannan jita-jita ta sahihin shafinsa na Instagram a yau Alhamis, inda ya ce mawallafin da ke yaɗa jita-jitar ya ɗauki hotunansa ne daga wani fim da ya yi kwanan nan a Ghana. Daily Nigerian na ruwaito
“Jama’a, ya zama dole na magantu a kan wata jita-jita da ke ta yawo a baya-bayan nan. Yawancin lokaci, ban fiye maida hankali na kan irin waɗannan jita-jita ba sabo da ba sa ɗaɗani da ƙasa. Amma bai kamata a ketare wasu layukan ba,” inji shi.
“Na yi wani fim wata ɗaya da ya wuce a Ghana game da wani mai kishin addini. Shi ne wani ya ɗauki hotuna daga wannan fim ɗin kuma ya ƙare a hannun wani ja’irin marubuci ta yanar gizo. Duk da yake ba ni da wata matsala game da kowane addini, ba ni da niyyar, canza addini a yanzu koma kwata-kwata a rayuwa ta.
“Ban fahimci dalilin da yasa kowa zai so yin wannan jita-jita ba amma akwai wasu layukan da bai kamata a ketare ba. Don haka duk wanda ke tallar wadannan jita-jita to shi ta shafa. Mu harkokin gaban mu mu ka sanya a gaba,” in ji Iyke.
Kalli bidiyon a Nan.
View this post on Instagram