Uncategorized
Hotunan Bikin Auren Dan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Advertisment
Gwanin Ban Sha’awa
Daga Habibu Aja’waya Dawakin Dakata
Hakika hotunan Auren ASP Aminu Sanusi Babban dan mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da amaryarsa Zainab Ali Bashir, sune hotunan da ya kamata a ce dukkan ma’aurata hade da ya’yan manyan kasa na yin irinsu, domin bawa al’adarmu ta Hausa/Fulani fifiko tare da inganta ta.
Ko shakka babu na san za ku yi alkalanci idan har ku kaga yanayin daukar hotunan, tare da shigar da ango da amaryar suka yi, musamman ganin yadda wasu ma’auratan a wannan zamanin ke yin yadda suka ga dama wajen daukar hotuna barkatai a yada a duniya.
Advertisment
Muna rokon Allah ya sanya alkairi ya ba su zaman lafiya tare da zuri’a dayyiba, amin..
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com