Uncategorized
FATAWAR RABON GADO (64)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA
FATWAR RABON GADO (64)
Tambaya?
Assalam alaikum,
MACE TA MUTU TA BAR: 1.MIJI 2.MAHAIFIYA 3.’YAR UWA SHAKIKIYA 4.’YAN UWA MAZA DA MATA UWA DAYA 5.’YAN UWA UBA DAYA MAZA DA MATA ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI MALAM
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ta bari gida: 9, (Auli daga shida) a bawa miji kashi: 3, sai a bawa uwa kashi: 1, ‘yar’uwa shakikiya za ta dauki kashi:3, sai a bawa ‘yan’uwan da aka hada uwa daya kashi biyun.
Allah ne mafi Sani.
8/10/2016
Amsawa: Dr Jamilu zarewa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.


