Wani Ango Ya Saki Amaryarsa Bayan Sa’a Daya kacal Da daura aurensu A Saudiyya
Taura – Aure na daga cikin abubuwa masu muhimmanci a rayuwar mutum. Burin duk wanda ya yi aure shine babu rabuwa sai dai idan mutuwa ce zata raba – Rahotannin sun bayyana cewar wani Ango a kasar Saudiyya ya saki amaryarsa bayan sa’a daya kacal da adaura masu aure – Jama’a sun yi matukar mamakin halayyar wannan Ango, bayan ya furta hau sau uku a gaban jama’a cewar ya saki amaryarsa Aure na daga cikin abubuwa masu muhimmanci a rayuwar mutum.
Burin duk wanda ya yi aure shine babu rabuwa sai dai idan mutuwa ce zata raba. Yanzu dai wani aure da ya mutu tsananin wani Ango da Amaryar sa ya shiga tarihi a matsayin aure mafi gajarta a duniya. Rahotannin sun bayyana cewar wani Ango a kasar Saudiyya ya saki amaryarsa bayan sa’a daya kacal da adaura masu aure. Ango da amarya Source: Facebook Jama’a sun yi matukar mamakin halayyar wannan Ango, bayan ya furta hau sau uku a gaban jama’a cewar ya saki amaryarsa. Angon bai tsaya iya nan ba sai da ya umarci jami’an gwamnati da suka halarci taron biki cewar su shaida cewar babu aure tsakaninsa da sabuwar amaryar tasa.
Kafar yada labarai ta Sabq da ta rawaito labarin, ta ce angon ya dauki wannan mataki ne bayan mahaifiyar sa ta kafe a kan ya rabu da amaryar tasa ya kuma gimtse duk wata mu’amala da ita. Ango da Amaryar sun hadu ne yayin karatu a wata jami’ar kasar waje. Sai dai bayan an mahaifiyar angon da ‘yar uwar sa sun ga amaryar bayan an daura aure, sai suka nuna rashin amincewar su da aurenta. Mahaifiyar angon da ‘yar uwar sa sun ki amincewa da auren ne bayan gano cewar amaryar ta fito daga wata kabila ce daban da tasu.