Labarai

Ana kukan targade: An samu bullowar wata sabuwar kungiyar mai suna “Hakika” a arewacin Najeriya

Advertisment

Hukumar sojin Najeriya ta bakin Laftanal TG Iortyom, mukaddashin kwamandan rundunar Ofireshon lafiya dole, mai aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno ta sanar da bullowar wata kungiya mai suna “Hakika”. Sanarwar ta bayyana cewar kungiyar ta bullo ne a yankin kananan hukumomin Yola ta kudu a jihar Adamawa da Toto a jihar Nasarawa. 

Buratai Iortyom ya kara da cewar yanzu haka kungiyar karkashin jagorancin Yahaya Ibrahim na daukan dirbobi tare da gindaya masu wasu sharuda da suka hada da daina yin sallah biyar (5) a rana, daina yin azumi da daurewa zina gindi.

 Hukumar soji ta bukaci ragowar hukumomin tsaro da su saka ido a kan harkokin kungiyar a wuraren da suke aiki da kuma bukatar jama’a su sanar da hukuma harkokin duk wata kungiya ko mutane da basu yarda da shi ba. 

Sources: Naijhausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button