Kwalbar pepsi tana son zamo silar mutuwar aure


Majiyarmu ta samu wani labari mai dauke da darasi wanda tabbas a rayuwar mu duk abinda kaga anyi maga rangwame ka daina kushewa wani makami mai suna Sukairaj Hafiz Imam mai amfani da kafar sada zumunta ya wallafa wanann labarin.
Wani Saurayi yaje neman auren wata Budurwa. Ko da Mahaifinta ya yi bincike akansa sai ya same shi mutumin kirki ne kuma mai tarbiyya.
Mahaifinta yace bama tsanantawa a harkar aure, ba abin da muke buƙata in ba ku zauna lafiya ba. Kaje ka kawo Dinare ɗaya ya wadatar.
Saurayi ya yi murna sosai. Bayan an ɗaura aure, in mijin yana cikin nishaɗi sai ya siyo kwalba ɗaya ta lemon Pepsi, sai ya kalli matar sai ya ce, da ke da wannan lemon farashinku ɗaya, duk Dinare 1 ne.
Matar tana jin haushin abin da mijinta yake yi mata amma tana danne fushinta, bata bayyanawa. Mijin sai ya koma kiranta da “Kwalbar Pepsi”
Da abin ya dameta sai ta ce, zata je wajen Iyayenta, ko da zuwanta sai t ce, kun karya mini farashi, kun bada ni a wulaƙance, ga shi nan mijina yana ci mini mutunci, saboda rangwame da kuka yi masa wajen biyan haƙƙin aure.
Iyayenta suka yi fushi sosai. Mijinta yazo ɗaukarta don su tafi gida, sai mahaifinta ya ce, ka yi haƙuri k barta ta kwana a nan, zata tayamu aiki, gobe muna da walima. Ka faɗawa Iyayenka ina gayyatarsu, kai ma kuma haka… Saurayi ya yi murna sosai..
Da safe suka shirya shi da Iyayensa suka je. Ko da zuwansu sai Mahaifin yarinyar y ajiye musu kwalba 3 ta lemon Pepsi, ya ce, kun karbi ƴata da kwalba ɗaya ta Pepsi, saboda karamci yanzu na baku Uku na karbi Ƴata….!
Iyayen saurayi ba su fuskanta b amma shi kuwa ya durƙusar da kai, saboda tsananin jin kunya ji yake kamar ya nitse a ƙasa.
Mahaifin yarinyar ya yiwa iyayenta sharhin abin da ya faru daga farko har ƙarshe. Suka yi Allah wadai da abin da ɗansu ya aikata, suka yi ta bawa mahaifin yarinyar haƙuri..!
Mahaifinta ya ce, na haƙura amma wallahi ba zata koma ba sai y biya Dinare DUBU HAMSIN ko kuma a raba auren. Yanzu kam, duk abin da ake yiwa Ƴa a aure nima sai an yiwa tawa…!
Iyayen saurayi suka ce, wallahi gaskiyarka, muma mun goyi baya. Haka aka lalubo kuɗi aka kawo sbd yana ƙaunarta.
Da shigowarta gidan, sai ya kalleta cikin murmushi ya ce, Masha Allah “Kamfanin Pepsi ta dawo…!”