Ba Zan Taba Neman Gafara Ga Shugaba Muhammad buhari ba inji Buba Galadima
Daya daga cikin jigogin da aka kafa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, tare da kasancewa na gaba-gaba wajen fafutukar ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya samu mulkin Najeriya, Injiniya Buba Galadima, ya ce bai gamsu da kamun ludayin gwamnatin ba.
A hirarsa da BBC Buba Galadima ya ce a yanayin salon jagorancin jam’iyyar da kuma mulkin da ake yi a kasar a yanzu, lamarin ya ba su mamaki domin sun yi zaton za a samu gagarumin sauyi a kasar zuwa yanzu, amma hakan ba ta kasance ba.
Ya ce abin takaicin shi ne Allah ya jarrabi Shugaba Muhamadu Buhari da rashin lafiya, kuma dadin dadawa sai jam’iyyar ta kasa samar da wani kyakkyawan shugabanci, wanda duka wadannan abubuwa sun shafi yanayin mulkin.
Game da rashin ba shi wani mukami ko tafiya da shi a gwamnatin Buharin, Buba Galadima ya musanta cewa akwai wani sabani a tsakaninsu da Shugaban, wanda ake rade-radin cewa saboda hakan ne ba a tafiyar da shi.
Ya ce a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka assasa tafiyar har ta kai an kafa gwamnati ba ya bukatar har sai ya yi kamun kafa, ko wani tumasanshi a wurin Shugaba Buhari kafin a san da shi har a ba shi wani mukami.
Injinyan ya ce rashin ba shi mukami bai dame shi ba, domin kusan duk wadanda suka faro tafiyar tabbatar da kasancewar Buharin ya zama shugaban kasa, babu wanda aka ba wa wani mukami.
Don haka ce shi ba komai ba ne, yana mai shagube da cewa: ”Ni ai a cikin miya ban kai komai ba.”
Kawo yanzu babu wani martani daga bangaren Shugaba Buhari ko kuma jam’iyyar APC.
Dan siyasar ya dangantaka ba shi mukami ga lamari na Ubangiji, yana mai cewa duk abin da mutum ya samu Allah ne, haka kuma in mutum ya rasa Allah ne, amma ba ya nadamar gwagwarmayar tabbatar da Buhari Shugaban kasa, don bai samu mukami ba.
Ya ce ba wata gafara da zai nema daga Shugaban, ko zai waiwaye shi da mukami, domin shi a saninsa ba wani abu da ya yi na sabamasa.
Game da dantakarar da Buba Galadiman zai mara wa baya a zabe na gaba na 2019, ya ce lokaci bai yi ba tukuna, amma idan lokacin ya zo zai karkata ga ra’ayinsa, ko da kuwa za a kashe shi ne.
Sai dai ya ce in har Buhari ya neme shi a tafiyar 2019, idan zai yi takara zai iya mara masa baya, amma ba wai haka kawai ya kai kansa tafiyar ba, ba tare da an gayyace shi ba.
Amma ya ce ko a yanzu Buhari ya kirawo shi ya ba shi mukami zai karba, domin magana ce ta kokarin ciyar da kasa gaba da yi wa al’umma hidima, amma ya wuce a ce ya je ya nemi a ba shi aiki a gwamnatin