Yadda na dawo da budurwar mijina gidana don mu ci gaba da faranta masa rai tare – Matar aure
Wasu mata biyu a kasar Kenya sun bayyana yadda yanzu haka suke zama a gida daya tare da mijinsu, Abraham, Labarunhausa ta ruwaito.
Sarah da Maureen suna zama ne a matsayin kishiyoyi bayan Abraham ya auresu gaba daya, kuma suna nuna wa juna so da kauna tamkar ‘yan uwa.
Yayin da uwar gidan take bayani, ta ce da farko ta gano yadda mijinta da Maureen suke yawan tuntubar juna a lokacin Maureen tana da cikin danta na farko.
Hakan yasa daga baya ta fuskantar mijinta don jin yadda ya ci amanarta har ta gano wasu hotunan dan da Maureen ta haifa a wayarsa.
Daga nan ne ta cije ta fuskance shi don jin ta bakinsa akan alakar da ke tsakaninsa da Maureen.
“Na gano ne bayan diyata ta nuna min hoton jariri a wayarsa. Daga nan na fara bincike har na gano ashe har haihuwa ya yi da Maureen,” kamar yadda ta bayyana.
Abraham bai musanta batun alakar da ke tsakaninsu ba da kuma dan da suka haifa tare. Sarah ta ce ta yi mamaki, amma bayan ya tabbatar mata da gaskiyar lamari sai ta amince kuma bata yi yunkurin rabuwa da mijinta ba.
Bayan watanni kadan da gano Maureen, Sarah ta yi kokarin ganawa da ita inda ta amince da ta dawo gidan da take zama a matsayin kishiyarta.
Ta ci gaba da cewa:
“Mijina ya rakani har gidanta inda ma gana da ita a karon farko. Ta bude mana kofa inda ta gaisheni bayan ta ganni a gaban mota.”
Yadda suka fara zama tare a matsayin kishiyoyi
A cewarta, suna jin dadin zama a matsayin kishiyoyi yanzu haka tare da mijinsu da yaransu. Kuma sun fara ne da fitar da yaransu a ko wanne mako, ranar Lahadi don su yi wasanni.
Su kan dade acan har su kai dare, hakan yasa wani lokacin suke kwana a gidan da mijin ya ajiye Sarah. Bayan an dauki lokaci mai tsawo ana hakan sai Maureen ta dawo gidan gabadaya.
Yanzu haka shekararsu daya da rabi suna zama tare a gida daya. Kuma yaransu sun shaku kwarai sannan suna matukar kaunar juna.
Mauren ta bayyana yadda ta fara tarkato kayanta a hankali har ta gama kwashe su zuwa gidan. Suna matukar kauna da mutunta juna a matsayin kishiyoyi, kawaye kuma ‘yan uwan juna.
Batun kwana kuma, sun ce ko wacce tana da dakinta kuma mijinsu ne yake zaben dakin da zai kwana a ko wanne dare.
Yanzu haka dan Maureen daya yayin da Sarah ke da yara uku.