Wasanni: Ronaldo ya fi kowa karbar kudi a wasanni a duniya
– Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya ci gaba da zama a matsayi na daya a wanda ya fi karbar albashi a tsakankanin masu wasanni a duniya in ji mujallar Forbes.
– A bara Ronaldo ya karbi fam miliyan 72.05 kudin albashi da ladan wasanni da tallace-tallace da ya yi, amma a bana ya samu karin fam miliyan 3.87.
Cikin jadawalin da Forbes ta fitar ‘yan wasa 11 ne daga wasanni daban-daban suke kan gaba a wajen samun kudi.
Masu wasan kwallon kwando su 32 ne suke cikin 100 farko, sai masu buga kwallon baseball 22 da ‘yan wasan zari-ruga na Amurka 15 da masu taka-leda tara.
NAIJ.com ta samo jerin ‘yan wasa 10 da suka fi samun kudin a duniya:
1.Cristiano Ronaldo – kwallon kafa ($93m/£72.05m)
Wasanni:
2.LeBron James – kwallon basketball ($86.2m/£66.79m)
3.Lionel Messi – kwallon kafa ($80m/£61.98m)
4.Roger Federer – kwallon tennis ($64m/£49.58m)
5.Kevin Durant – kwallon kwando ($60.6m/£46.95m)
6.Andrew Luck – zari-ruga ($50m/£38.74m)
7.Rory McIlroy – kwallon golf ($50m/£38.74m)
8.Stephen Curry – kwallon kwando ($47.3m/£36.64m)
9.James Harden – kwallon kwando ($46.6m/£36.10m)
10.Lewis Hamilton – tseren motoci a($46m/£35.64m)