Kannywood

Jaruma Hadiza Gabon Ce Zakaran Gwajin Dafi A Masana’antar Kannywood

Hadiza Gabon: Yabanya, Allah Ya Fisshe Ki Fari

Daga : ASHAFA MURNA I [email protected]
Ban taba ganin Hadiza Gabon ido-da-ido ba, ban kuma taba yin waya ko gaisuwar sakon text da ita ba, duk kuwa da cewa na yi wa ‘yan fim kyakkyawan sani, su ma sun san ni ba sanin shanu ba. Domin a tsakanin shekarar 2000 zuwa yau, na yi hira da ‘yan fim sun fi 100 daya.


Abin da ba ka sani ba, wuyar kwatance gare shi. Duk da haka ba zai hana ni yin kwatancen halayyar Hadiza Gabon da ta wasu fitattun jaruman fina-finai da mawaka ba. Mai yiwuwa yin haka zai sa mai karatu ya fahimci inda na nufa.

Kamar Gabon kamar fitacciyar matashiyar mawakiyar nan Tailor Swift, wacce rudin duniya bai kwashe ta ya mantar da ita daga tallafa wa gajiyayyu da mabukata ba. Ko a cikin shekarar nan sai da Swift ta ceto wata mawakiyar da furodusa ya yi mata kan-ta-waye, ya tsiyata ta karkaf.
Tallafin naira milyan 90 da Swift ta ba Kesha ya farfado da ita daga mawuyacin halin da ta shiga a lokacin da ta ke ta fadi-tashin shari’a da furodusa dan kan-ta-waye, Dakta Lukas a kotu, a Amurka. Haka cikin watannin baya sai da ta yi alkawarin bayar da tallafin naira milyan 370 a matsayin gudummawa ga ambaliyar da aka yi a garin Louisiana, a Amurka.

Kamar Gabon kamar Miley Cyrus, mashahuriyar mawakiyar nan da ta yi fice a kidan garaya. Ganin yadda a ‘yan shekarun nan ta ke ta sadaukar da kudin ta wajen tallafa wa mabukata, an tambayeta dalilin yin haka. Sai Cyrus ta ce: “Jama’a tun fa ina ‘yar shekara takwas na ke kada garaya ina samun kudi. Tunda har na kai shekara 20 a duniya, idan ban fara bayar da taimako da tallafi ba tun a yanzu, me zan yi da kudin? Kuma ni tun ina kankanuwa haka na ga iyaye na su na yi”
Kamar Gabon kamar kasaitaccen attajirin dan fim George Lucas, mai fina-finan Star Wars. Lokacin da Lucas ya saida finafinansa ga kamfanin Disney har Dala Bilyan hudu, sai ya yi ta kamfatar kudin ya na bayar da tallafi ga kungiyoyin taimaka wa marasa galihu a duniya. “Yanzu na kai munzulin fara gajiya da adana kudi. Shekara 41 ina tattalin kimshe kudi a banki. Na fara gajiya haka nan, ya kamata mabukata su fara amfana da ni.” Inji George Lucas.

Kamar Gabon kamar Angelina Jolie. Ita wannan jarumar a yanzu duk duniya an san yadda ta ke gaganiyar taimaka wa ‘yan gudun hijira da kuma kananan yara. Har marayu ta kan dauka ta maida su ‘ya’yanta. Jolie tana a sahun gaba na wadanda Majalisar Dunkin Duniya ke tinkaho da ita.

Kamar Gabon kamar Emma Watson, jarumar “Harry Potter and the Deathly Hallows”, wacce baya-bayan nan ta bai wa jami’o’i goma tallafi.

Kamar Gabon kamar Ian Somerhalder, jarumin “Vampire Diaries”, wanda Allah Ya bai wa tausayin dabbobi, kuma ya ke kashe kudin sa wajen tallafin kula da dabbobi marasa lafiya da ke watangaririya a jeji.

Kamar Gabon kamar Beyonce, mawakiyar nan da kusan kowa ya sani, wacce jim kadan bayan madatsar ruwa ta birnin Michigan da gurbace da guba, nan da nan Beyonce ta hada gagarimimar kalankuwa, inda ta sadaukar da kudin wajen gaggauta aikin tace gubar da ta gurbata ruwan.


Hadiza Aliyu Gabon, wacce ta fara fita a finafinan Hausa cikin 2009, a fim din “Artabu”. A yau ta zama abin kwatance, abin alfahari, abin godiya, abin tinkaho kuma uwa, uwar daki da kuma sarauniyar gajiyayyu. Ba don komai ba sai don irin yadda ta ke sadaukar da lokacin ta da dukiyar ta wajen taimaka wa makwabta da kuma musammam tallafin jin kai da ta ke yawan bayarwa a sansanin ‘yan gudun hijira, wanda ko a kwanan nan sai da ta yi haka a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira da ke Wudil, a Jihar Kano.


A wannan lokaci da ake fafutikar nema da tara kudi bakin-rai-bakin-fama, lokacin da yawanci wanda ya samu ko ya dai jida ya tara a banki, ko kuma ya kimshe ko ya maida su kadara, an samu wata matashiyar yarinya da duk da cewa ta na da zafin nema, hakan bai hana ta diba ta na bayarwa ga inda ya dace a bayar ba. Ga shi kuma har Gidauniyar Ciyarwa Lokacin Azumi ta kafa.


A ranar 1 Ga Yuni, 2017 ne Gabon ke cika shekara 28 a duniya. Ni ma tashi na yi da safe na ga ana ta yi mata fatan alheri a cikin kafafen sadarwa na Facebook da Instagram. Shi ya sa na ce zan yi mata fatan alheri, amma har da hadawa da yaba irin halayyar ta.


Gabon, Allah Ya sa ki gama da duniya lafiya. Duk wani wanda tauraronsa ke haskawa, wannan ne fatan da masoyansa ke yi masa. Ke ma na san addu’ar da ki ke yi wa kan ki kenan, irin addu’ar da mashahurin mawakin Hausa, Marigayi Musa Dankwaro ya yi wa kansa, a cikin wakar Sarkin Kayan Muradun, Marigayi Muhammadu Tambari:

“Daukan ni duniya kwarai,
In dai za ki aje ni,
To aje ni sannu kak ki kasan,
Don wani da nig ga ta kasai,
Ya kalle wuya,
Ya kalle ga tsara,
Ya kalle ga hannu,
To halin ki duniya an nan,
Wani ta yi mai cin-bulak-kuturu,
Ya hwada miya da yafki.”
ASHAFA ma’aikaci ne a Premium Times Newspaper, Abuja.
08036890400.
© Zuma Times Hausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button