Kannywood

Sabon Salo Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Shirya Fim Mai Suna “Yaki A Soyayya”

Advertisment


A kwanakinnan ne Nafisa Abdullahi ta fitar da wani Samfurin wakar Sabon fim dinta mai suna Yaki A Soyayya; fim din wanda kafin yanzu ana kiransa da suna Karma ya hada fitattun Jarumai irinsu Abdul M Shareef, Nafisa Abdullahi, falalu Dorayi, Bilkisu Abdullahi da dai sauransu.

A wata hira da manema Labarai Nafisa ta bayyana cewa kafin shirya fim din sai da Aljihunta ya Girgiza ma’ana ta kashe kudade da yawa, ta kara da cewa fim din ya qara fito da wata baiwa tata wadda ita kanta bata san tana da ita ba sannan ta samu fasahar kirkiro labarin ne yayinda take kallon wani fim, kuma tayi aikin Daukan shirin ne a garuruwan Abuja da Lagos
Nafisa Abdullahi hakika babbar jaruma ce da ta shafe shekaru da dama a masana’antar kannywood ta kuma lashe kyaututtuka masu tarin yawa daga ciki da kuma wajen kasar nan.

Daga karshe ne kuma ta kara tabbatar wa da magoya bayan ta cikakkiyar kaunar ta agare su tare da shan alwashin cigaba da kayatar da su a cikin fina-finan ta.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button