Kannywood

Hukumar tace fina finai ta yi martani kan masu sukar tsarin na sabunta rijistar yan Kannywood

Hukumar tace Bata dau wannan mataki ba Saida ta zauna da dukkan bangarorin da suke da ruwa da tsaki a masana’antar dangane da yin hakan a inda daga karshe suka cimma matsayar sabunta rigistar a karkashin manyan Kungiyoyin masana’antar Wanda suka hada da : MOPPAN, AREWA FILM’S MAKERS DA KANNYWOOD ELDERS FORUM.

Hukumar tace, kadan daga cikin manufar sabunta rigistar shine, fidda bara gurbi a tsakankanin yan masana’antar, Sai Kuma son sanin adadin suwaye halattatun Yan masana’antar a wani kudi guda daya ta yadda gobnati da sauran Hukumomi da suke son yin aiki da masana’antar zasu sami damar yin hakan in bukatar hakan ya taso. Baya ga sauran ran mayan dalilan da suka shafi tsaro da tarbiyya.

Hukumar ta Kara da cewa , masu kalubalantar tsarin suna yine saboda wata manufa ta kashin kansu ba Wai Suna yine da yawun yan masana’antar ta kannywood ba.

Idan ba’a mantaba Hukumar tace Fina-finan ta kawo abubbuwan cigaba da yawa Kamar nemawa Yan masana’antar hakkin su a gurin Hukumomin gobnatin tarayya irinsu Hukumar copyright Commission baya ga kulla alaka tsakanin yan masana’antar ta kannywood da Hukumar lura da Tallace- Tallace ta kasa wato (APCON) Sai shiga tsakani dangane da rashin fahimtar dake faruwa a cikin masana’antar ta kannywood inda aka samu dai-daito musamman akan abinda ya shafi masu sana’ar downloading da masu fassara Fina-finan waje zuwa Hausa.

Hukumar ta Kara da cewa, ko a baya-bayan nan tayi nasarar dawo da masu sana’ar gidajen kallo karkashin kulawar ta tare da kafa musu sharuda ciki ko harda dawo da Haska Fina-finan Hausa duk domin a farfado da masana’antar ta kannywood.

Amma abun takaici masu kalubalantar Hukumar basu taba yaba mata ba duba da wannan tarin Nasarori cikin kankanin lokaci.

Abdullahi Sani Sulaiman
Jami’an Hulda da jama’a na Hukumar tace Fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button