Kannywood

Yadda Wakokin Fim Din Mansoor Suka Samu Karbuwa Tun Kafin Su Fita


A kwanakin baya ne shahararren kamfanin shirya finafinan Hausa FKD, ya fitar da taba ka lashen sabbin wakokin fim dinsa mai suna Mansoor, wadanda yanzu haka suka yamutsa hazo a farfajiya Kannywood, duk da cewa ba a fitar da su kasuwa ba.

Da yake zantawa da wakilinmu game da yadda wakokin suka samu karbuwa a zukatan al’umma, wani darakta da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce hakika idan ana batun zuwa da wakoki masu dadi a cikin finafinan Hausa, to kamfanin FKD shi ne kan gaba wajen ganin ya zo da dadadan wadodin masu sanyaya zuciyar mai sauraro.

“Kamfanin FKD ya yi kaurin suna ta wannan bangaren tun shekaru da dama da suka gabata. Domin sun fitar da wakoki wadanda har yau din nan an kasa mantawa da su irinsu: Mujadala, Fil’Azal, Sai Wata Rana, Madubin Dubawa, Adamsy, Sirrin Da Ke Raina, Halacci, Halwa da kuma baya bayan nan Gamun Nan Dai.” In ji shi.

Wannan karon kamfanin ya sake zuwa da wani salon na daban, wanda za a iya cewa shi ne irinsa na farko a cikin wani sabon shiri mai suna MANSOOR. Wakokin fim din; Abin Da Yake Raina, Zan Rayu Da Ke, Makullin Zuciya, Macukule, Jirgin So Zai Tashi da Ya Mansoor Na, tuni sun hau kan kadamin zamowa shahararru da za su dade a kunnunwa masoya.

Hakika Umar M Shareef, Abdul D. One, Murja Baba, Maryam Fantimoti, da Khairat Abdullahi da suka bada muryoyinsu wajen rera wadannan wadodi na madaukakiyar soyayya sun taka rawar gani. Da ma me ake tsammani daga wurin mutanen da suke da tarin basira wajen sarrafa murya don yi wakar soyayya? Bari mu dan kalli wakokin don yin bayani a kansu…

Abdul D. One (Marubucin Waka kuma Mai Rerawa), ya yi amfani da muryarsa wajen rera wakar ‘Abin Da Yake Raina’ da a yanzu samari da ‘yan mata ke yin guzurinta don farantawa juna rai. Tabbas dadin wakar ya kai matsayin da idan mutum ya kunna sai dai ya yi ta ji ba tare da ya canja wata ba, saboda muryarsa tana da dadin sauraro. Maryam Fantimoti, ita ma ba a bar ta a baya ba, domin wakar da ta rera ‘Ya Mansoor Na’ tuni ta shiga sahun shahararrun wakoki ababen saurare.

Macukule,’ duk da ba irin wakokin da Umar ya saba yi ba ne, amma ya yi matukar kokari tun daga farkonta har karshe. Babu wani sabon abu a cikinta, amma tsarin kid’anta ya yi matuk’ar dadi. Har ila yau, lafuzan da aka yi amfani da su sun tsaru tsaf, ta yadda za a nishadantar da mai sauraro. Hakika idan wakar ta samu talla sosai, za ta zamo daya tamkar da dubu a wurin masoya sauraron waka.

Fitar wakar ‘Zan Rayu Da Ke ’ ya sauya salon album din gaba daya, domin Umar M. Shareef ya kara nuna wa duniya cewar indai bangaren wakar soyayya ne to ba shi da na biyu. Duk wani masoyi, ko masoyiya, zai so a ce shi ake rerawa wannan waka. Tuni ya sanya hatta manyan jaruman a Kannywood da sauran mutane rera wakar suna dora ta a shafukansu na Instagram, yayin da jarumi Ali Nuhu ke bayyana farin cikinsa da zarar sun yin hakan.

‘Jirgin So Zaya Tashi’ wadda Umar suka rera tare da Murja Baba ta yi dadi matuka, hakan yana kara bayyana basirar mawakin a fili. Kidan ya tsaru matuka, zubin tsarin zantukan da aka yi amfani da abun burgewa ne. Kai da nemi wakar kawai ka saurara.

Makullin Zuciyata ’ irin wakokin nan ne da idan mutum ya fara saurara shi kenan sun shiga jikinsa, batun dainawa ma sam bai taso ba. Waka ce da ke bayyana irin yadda masoyi ya kamu da son masoyiyarsa, da kuma irin fatan da yake da shi na ganin ta karbi soyayyarsa da hannun biyu.

Wadannan su ne wakokin da fim MANSOOR yake dauke da su. Ana sa ran fitarsu nan ba da jimawa ba.
Babban abinda aka fi mayar da kai yanzu haka shi ne, yanayin yadda labarin fim din zai kasance, domin an ga mawaki Umar M. Shareef ya yi tsalle tare da fadowa duniyar jarumai don a dama shi. Ganin Umar cikin fim din ya sanya masoya zuba ido, suna jiran ganin yadda zata kaya.

Labari: Ali Nuhu
Tsarawa: Jamil Nafseen
Rubutawa Waka: Umar M Shareef, Abdul D One
Rerawa: Umar M. Shareef, Abdul D. One, Maryam Fantimoti, Murja Baba da Khairat Abdullahi.

Koyar Da Rawa: Ali Nuhu

Shiryawa: Nazir Dan Hajiya

Bada Umarni: Ali Nuhu

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button