Kannywood

An Gurfanar Da Mustapha Naburaska a Gatan Wata kotu A kano

 
Mustapha Naburaska, daya daga cikin fitattun jaruman dandalin Kannywood, a karshen makon da ya gabata ya fada komar kwamitin tsaftar muhalli da Gwamnatin Kano ta kafa.
Jarumin wanda mazauni ne a Unguwar Tudun Wada ta Karamar Hukumar Nasarawa da ke Birnin Dabo, ya tsinci kansa a gaban kotun tafi-da-gidanka bayan ya keta dokar kwamitin tsaftar muhalli wadda ta hana fita har sai karfe 10.00 na safiya a duk ranar Asabar ta karshen kowane wata.
Naburaska yayin zantawa da manema labarai na Gidan Rediyon Freedom, ya ce rashin sani ya sanya ya fito domin halartar wata jana’iza kuma a yanzu ya fahimci cewa tsaftar muhalli ta kore kowane uzuri.
Kotun ta nemi Jarumin ya biya naira dubu biyar a matsayin tarar keta dokar zama a gida domin tsaftace muhalli inda ya nemi rangwami kuma ta yi masa sassaucin biyan naira dubu uku.
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button