Uncategorized

Soyayya ko hauka: Tsananin soyayya ta saka budurwa sato akuyar makwabta ta yanka ta yiwa saurayinta farfesu

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta zama abar kwatance a shafin sadarwa na Twitter bayan ta bayyana irin abinda tayi a rayuwarta saboda soyayya

– Budurwar wacce ta bayyana sunanta da Adejoke, ta bayyana cewa ta yiwa saurayinta da abokanan shi farfesu da akuyar sata

– Adejoke ta ce ta yiwa saurayin nata wannan abu ne saboda ta san cewa wata rana zasu yi aure tare

Wata budurwa da ta bayyana sunanta da Adejoke ta zama abar magana a kafafen sada zumunta, musamman ma shafin Twitter, bayan ta bayyana irin abinda tayi saboda soyayya a lokacin da take dalibar jami’a.

Budurwar ta bayyana wannan labari nata ne a shafin na Twitter, bayan an wallafa wata tambaya da ake kowa ya bayar da tarihin abinda yayi akan soyayya.

A cewar Adejoke, lokacin da take jami’a ta yadda a zuciyarta cewa saurayinta da suke soyayya a wancan lokacin zai aureta. Ta ce domin ba za ta iya mancewa ba hatta abokanan shi suna kiranta da matar mu ne, inda suke gaya mata cewa tafi tsohuwar budurwarshi.

Adejoke ta bayyana cewa abinda tayi wanda baza ta taba mantawa a rayuwarta ba shine yadda ta dafa akuya sukutum ta kaiwa saurayinta da abokanan shi.

Majiyarmu ta samu  daga legit, Ta cewa akuyar da ta dafawa saurayin nata ta sata ce, sannan budurwar ta kara da cewa a lokacin har wanki take yiwa saurayin nata na kayanshi na sawa.

A cikin labarin da Adejoke take bayarwa ta bayyana cewa yanzu haka tsohon saurayin nata yaje ya auri waccan tsohuwar budurwar tashi da abokanan shi suke cewa ta fita.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA