Uncategorized

Maganganu 6 da shugabannin Arewa sukayi akan Buhari

Malajisar dattawan Arewa sun yi wata taro na zaman dattawan arewan a ranan Litinin, 10 ga watan Oktoba a jihar Kaduna
– Manyan yan siyasa da shugabannin gargajiya sun halarci taron
– Wadanda sukayi magana a taron sune Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar da gwamnan jihar Borno mai suna Kashim Shettima

Buhari
Ga maganganu 6 da shugabanin arewa suka ce akan Shugaba Muhammadu Buhari
1. Shugabannin Arewan sunyi Magana akan Boko Haram
“Yau mun hadu a Kaduna cikin kwanciyan hankali , kuma a durkusar da boko haram. Shugaba Muhammadu Buhari ne mai ceton mu a arewa maso gabas, zuwan shi ta kawo karshen Boko haram.”
2. Sun ce Buhari ya karfafa tsaro: “Wasu zasu ce mun gode shugaba Buhari. Zamu iya cewa ka cika alkawarin ka na tabbatar da tsaro”
3. Sun tunantar da shi cewan mutane fan a cikin halin kunci da yunwa
“Bazamu hada kai da wandanda ke cewa shugaba Buhari ya daina tunatar da mu magabatan da suka jefa mu halin da muke ciki ba a yau. Amma zamu hada kai da masu tunatar da shi akan yunwan da yan Najeriya ke ji”.
4. Sun tunatar da shi cewan abubuwa na kara tsanani kullun
Hauhawar kudi na tsananta rayuwan jama’a kullun. Mutane na rasa ayyukansu. Kasuwani na durkushewa. Matasa na fidda tsammanin samun aiki. Asibitoci na cike da maras lafiya kuma basu da kudin jinya.”
5. Shugabannin Arewa sunce basuyi nadaman zaben Buhari ba
Masu kunne su ji, mutanen arewa basuyi nadaman zaben Buhari ba”
6. Sunce zasu kuma zaben shi a 2019
“In Allah ya kaimu 2019, zamu hada karfi da karfe domin sake zaben Shugaba Buhari. Zamu hada kai duk da bambancin addinin mu.”
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button