Uncategorized

Dandalin Kannywood: Korar Rahma yayi dai dai -Ali Nuhu

Jarumin finafinan Hausa Ali Nuhu ya bayyana goyaon bayansa ga korar da kungiya ta yiwa Rahma duk na ra’ayin cewa shi ya kamata a fara kora saboda irin abubuwan da yayi a finafinan turanci na Nollywood
– Mutane da yawa sun lakaba masa munafirci game da ra’ayoyinshi da ganin cewa su suka fara yin irin wannan laifin, kuma kungiya ta makaro a hukuncin ta ga Rahma
– Kungiyar MOPPAN ta ce ta riga ta ja layi, shi ya sa ta tauna aya domin tsakuwa ta ji tsoroKorar da kungiyar Motion Pictures
Practitioners Association of Nigeria
(MOPPAN) reshen jihar Kano ta yiwa jarumar finafinan Hausa Rahma Sadau na ci gaba da janyo ka-ce-na-ce.
Yayin da wasu mutane ke nuna goyon bayan hukuncin, wasu na cigaba da nuna rashin amincewarsu da korar da aka yi mata, wasu kuma ‘yan kadan daga kudanci wadanda abin da ta aikata ba wani abin kyama ba ne, na ganin cewa, tun da ta na bangaren masana’antar shirya finafinai na arewacin Najeriya ne, to dole ne ta bi ka’idar kungiya.
A hirarsa da jaridar Daily Trust Ali Nuhu, daya daga cikin jaruman finafinan Hausa, ya goyi da bayan hukuncin korar da aka yiwa Rahama, yana mai cewa: “a ganina wannan korar ta yi ma’ana, Ita ‘yar Kannywood ce, ta kuma fara aiki a Kannywood, kuma ta kaucewa da’a, da tsarin gudanarwa ta hanyar rike hannun namiji, da kuma hawa bayan mutumin.”
Mai aikin tsarawa, da kuma ba da umarni a finfinan Hausa, Ali Nuhu ya kuma kara da cewa, korar ta kasance mai tsanani ga laifukan da Rahama ta aikata na rungumar namiji, “Ba na zaton ta kamaci kora, kamata ya yi a dakatar da ita” , domin a cewarsa, akwai yanayin da mutane ke hada manya da kuma kananan abubuwa, “Shi yasa ake son ayi zurfin tunani kafin a yanke shawara.”
Sai dai a kare matakin da kungiyar ta dauka, shugaban kungiyar na jihar Kano Kabiru Maikaba ya ce, sun yi zurfin tunani dakuma tafka muhawara mai zafi, kafin su kai ga yanke wannan hukunci na kora, ganin cewa wannan ba shi ne karo na farko da Rahma ta aikata irin wannan laifi ba, ana kuma yi mata gargadi amma ta ki ji.
Sai dai Ali wanda korar Rahma ta janyo masa cece-kuce, dangane da irin rawar da ya taka a finafinan kudu, a inda ya ke rungumar ‘yan mata tare da sumbartarsu, bai ce komai ba da kiraye-kirayen da ake yi shi ma kore shi daga finafinan Hausa ba, sai da a wani hoton bidiyo na Sakataren kungiyar MOPPAN na Kano, Salisu Mohammed a lokacin da ya ke bayyana korar Rahma, ya na mai cewa, yanzu kungiyar ta ja layi dangane da irin abubuwan rashin da’a da ‘ya ‘yanta ke aikatawa.
Ita ma Rahma ta yi nadama a inda ta bayar da hakuri tare da neman gafara da laifukan da ta aikata, bayan da farko ta yi tirjiya, ta kuma yi ikirarin neman hakkinta a Kotu kamar yadda ta bayyana a shafinta na Facebook a intanet.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button