Uncategorized

DALIBIN DA YA YI AURE DA NIYYAR ŞAKI, IN YA GAMA KARATUNSA ?

DALIBIN DA YA YI AURE DA NIYYAR ŞAKI, IN YA GAMA KARATUNSA ?
Tambaya:
Malam shin ya halasta mutum ya je karatu wata kasar da Ba nasa ba zai yi shekara 5 sai yayi aure da niyan idan ya gama makarantan nashi sai ya sake ta, ya koma gida?
Amsa:
Wa alaikum assalam,wasu malaman sun halatta hakan,sai dai zance mafi inganci shi ne rashin halarcinsa,saboda ya yı kama da auran mutu’a, sannan kuma hakan ya sabawa wasu daga cikin manufofin aure, Kamar dawwamammar soyayya da kuma debe kewa,
Aya ta 21 a suratu Arrum ta tabbatar da cewa: an shar’anta aure ne dön ka nutsu da matar da zaka aura, wannan manufar ta goce a aure da niyyar saki.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa
.17/5/2016
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button