LabaraiUncategorized

Hotunan mawaki Grand P yayin da ya ke bayyana kaunarsa ga rusheshiyar budurwarsa

Guinea – Hausawa kan ce soyayya gamon jini. Babu shakka hakan ta ke ballantana idan aka duba lamarin fitaccen mawakin kasar Guinea, Grand P da kuma zukekiyar budurwarsa ‘yar asalin kasar Ivory Coast, Eudoxie Yao.
Duba da banbanci a girman jikin, mawakin dan tsurut ne amma budurwar ta sa shirgegiya ce, lamarin da yasa suka zama mutane biyu mabanbanta a bayyane.
Sai dai kuma da ya ke so gamon jini ne, sai ga shi mawakin ya wallafa hotunan shi da zukekiyar budurwarsa tare da kalamai masu dadi da tausasa zuciya.

A bayyane ya ke sanar da irin kaunar da ya ke mata tare da nuna yadda ya ke son ganin farin cikin ta.

Ina son ki kasance cikin farin ciki a kowanne minti da dakika. Ina kaunar ki sosai kuma ina farin cikin kasancewar ki a rayuwa ta. Ina fatan ki cigaba da kasancewa mai samar min da farinciki ya abar kauna ta,” ya rubuta.
Shege talauci, ina fatan Ubangiji yayi min tsari da shi: Bidiyon Melaye a jirgin Orji Kalu
Ke ce mafi girman mu’ujiza da ta taba faruwa da ni, mace mai matukar tsada, wacce na fi kauna. Ina son ki! Ina son ki! Ki saurari zuciya ta kuma ki kalle ni..
“Ba don ni ba, saboda mutunci na, na rantse zan yi miki biyayya. Babu abinda zai sauya kauna ta gare ki. Ubangiji ya kare soyayyarmu. Eudoxie Yao,” ya kara da cewa..
Kudajen zuma sun dinga harbin wani mutum yayin da ya ke turmi da tabarya da matar aure
A wani labari na daban, wani mutum daga kauyen Kwaramba a garin Gokwe na kasar Zimbabwe ya sha harbin kudajen zuma yayin da ya ke kwance turmi da tabarya da matar aure.
Kamar yadda Legit suka ruwaito, an tattaro cewa Jethro Maimba ya labe a daji inda ya kwanta da Lizzie Maphosa yayin da al’amarin ya faru.
Wani mazaunin kauyen da ya san yadda lamarin ya faru, ya sanar da B-Metro cewa kudajen zuman sun daina harbin Maimba ne bayan da ya roki yafiyar Musariri.

Grand p
Grand p

Grand p
Grand p

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button