Uncategorized

Mutumin Da Ake bi Azumin Ramadhan Zai iya azumin nafila a cikin goman farko naZulhijja?Dr. Muhd Sani Umar R/lemo

ODr. Muhd Sani Umar R/lemo
Azumtar Goman Zulhijja Ga Wanda Ake Bi Azumin Ramadan
Tambaya: Mutumin Da Ake bi Azumin Ramadhan Zai iya azumin nafila a cikin goman farko na
Zulhijja?
Amsa: Abin da ya
inganta na fatawoyin magabata cikin Sahabbai da Tabi’ai shi ne, duk mutumin da
ake bin sa azumin Ramadhana, to kamata yayi ya rama, maimakon yayi azumin nafila cikin wadannan kwanakin goma na Zulhijja. Wannan itace fatawar Abu Hurairah cikin sahabbai, da Ibrahim An-Nakha’i, da Sa’id bn Jubair, da
kuma Ata’ bn Rabah cikin tabi’ai.
1. Abdurrazzak As-Sana’ani ya ruwaito da
ingantacciyar salsala, daga Usman bn Mauhab, ya ce, na ji wani mutum ya tambayi Abu Hurairah
cewa, “Ana bi na wasu kwanaki na azumin
Ramadhana, shin zan iya azumin nafila a goman farko na zulhijja?” Sai Abu Hurairah ya amsa masa da cewa, “A’a. Saboda me? Fara da hakkin Allah tukuna, sannan daga baya ka azumci iya kwanakin
da ka ga dama”. [Al-Musannaf, Juzu’i na 4, shafi na 256, #7715].
2. Hammad bn Zaid, ya ce, Na tambayi Ibrahim An- Nakha’i da Sa’id bn Jubair game da mutumin da ake bi bashin azumin watan Ramadhan, shin zai iya
yin azumin tadawwa’i a cikin goman zul hijja? Sai su duka sukace  masa , ya fara da farilla
tukunna”. [Al-Musannaf, Juzu’i na 4, shafi na 256,
#7713].
3. Abdulmalik bn Juraij, ya ce, Ata’ bn Rabah ya
karhanta wa mutumin da ake bi bashin azumi na wajibi, yayi azumin nafila a wadannan kwanakin goma. [Al-Musannaf, Juzu’i na 4, shafi na 256,
#7716].
4. Kuma ya tabbata daga Umar Ibn Khattab cewa, yakan so ya rama azumin da ake bin sa a cikin
wadannan kwanakin goma.
5. Wasu daga cikin tabi’ai sun yi fatawa da hakan, kamar Ibn al-Musayyab, da Ibrahim An-Nakha’i.
[Duba Al-Musannaf, na Abdurrazzak, #7114, 9519,
9520].
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button