Labarai

Yan bindiga sun buɗe ma mota ɗauke da fasinjoji wuta a jihar Katsina

Advertisment

Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun bude wa wata mota ƙirar Golf mai dauke da fasinjoji fiye da mutum 10 wuta wanda mafi yawancinsu ‘yan yawon sallah ne a kan hanyar ‘Yan tumaki zuwa garin Ɗanmusa a jihar Katsina.

Katsina Reporters ta samu cewa, ‘yan bindigar ba su yi nasarar kashewa ko raunata kowa ba a cikin motar. Sai dai razani ya sa wasu daga cikin fasinjojin sun ji raunuka ya yin da suke gudun tsira.

A yanzu dai hanyar ‘Yantumaki zuwa Danmusa ta zama kabarin mutuwa wanda a kowace rana sai mahara sun tare hanyar sun ƙwashi mutane zuwa daji don neman kuɗin fansa.

Majiyar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:36 na ranar Asabar 13, ga watan Afrilu 2024 da muke ciki.

 

Wani Labari : Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Ta Ƙasa Na Shirin Tsunduma Yajin Aiki Ranar Laraba Mai Zuwa.

 

Kungiyar dillalan man fetur ta ƙasa IPMAN ta kuduri aniyar tsunduma cikin yajin aikin sai Baba ta gani a sati mai kamawa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Haka zalika Mambobin kungiyar sun ce za su kulle kowane gidan mai, saboda kin biyansu hakkokin su da Gwamnatin ta yi.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button