Lalurar nakasa: Labarin wani lebura mai kafa da ya dukufa wajen neman nakasan maimakon barace-barace


Wani mai larurar nakasa a Jihar Katsina, Yahuza, wanda aka fi sani da dan Nijeriya, ya shaida wa TRT Afrika yadda ya dukufa wajen neman na kansa maimakon yin barace-barace, yana mai cewa sau da dama yakan fi masu cikakkiyar lafiya iya leburanci.
TRT Afrika ta samu zantawa da wani bawan Allah inda tabbas kada ka yarda ka sayar da mutunci da kashi zuciyarka wajen neman abinda idan ka juya da baiwar da Allah yayi maka sai ka tsira da ranka, yahuza ya bayyana cewa :


“Sunana yahuza wanda anka fi sani da dan Najeriya a jihar katsina central market wannan lamari da rana tsaka ya same ni ina lafiya lau, amma da yake al’amarin Allah jarabta ce,gashi na dawo da kafa guda sanadiyar wannan hatsari da ya faru a mararabar safana .
An bashi shawara kuma nabi shawarar nan na jarabta na gani , sai na samu bacin rai ya fi yawa daga ciki , idan naje bara wani lokaci zan dawo cikin ɓacin rai, saboda irin abubuwan da muke fuskanta daga ciki, shi kenan naga in kuma leburancina.
Daman na iya aiki bakin gwargwado wasu in sun gani a haka da kafa guda wasu nacewa a diba ko wanne yayi nashi ana cikin wannan din sai su ga, su wanda za su yi ,da masu kafafuwa da wanda zan yi sai ta kasance daga cikin su na ma fi shi kokari a akan aikin, abinda zan yi shi ba zai iya ba.
Saboda akasin da su ke gane da shi haka kama aikin ni ba zan iya yi kamar yadda za su yi ba a tunaninsu amma sai an duba sai su ga kuma aikin da nake yi komai kafa biyu sai dai haka -inji yahuza dan Najeriya.
Ga bidiyon yahuza dan Najeriya
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




