Babu Wani Batun Karin Albashi Ga Ma’aikata A Ranar Independence -Gwamnatin Tarayya


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewar babu wani batun karin
Gwamnatin tarayya ta ce rahoton cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai sanar da bayar da albashin ma’aikata a ranar samun ‘yancin kai ba gaskiya bane.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta hannun Mista Olajide Oshundun, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar kwadago.shafin gidan tv Liberty kano na ruwaito a shafin na facebook.


Ministan Kwadago Na Najeriya Simon Lalong
Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton, yana mai jaddada cewa, kage ne kawai da yan media suka yi domin ya dace da labarin muradun da mediar ta fi sani.
An jawo hankalin Ma’aikatar Kwadago da Aiki kan rahotannin da ke yawo a yanar gizo na cewa Shugaban kasa zai ba da sanarwar bayar da kyautar albashi da kuma jin dadin ma’aikata yayin jawabinsa na ranar ‘yancin kai na ranar 1 ga Oktoba.
Rahoton wanda aka ce ya samo asali ne daga wata hira da aka yi da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, ya yi ikirarin cewa an shirya wani taro na karshe a ranar Talata tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ma’aikata don dakile yajin aikin da ake shirin yi.
Muna so mu bayyana a fili cewa rahoton karya ne kuma yaudara ne kamar yadda babu wani lokaci da Daraktan Yada Labarai ya bayyana irin wannan in ji shi.
Ya kara da cewa, don kawar da shakku, yana da muhimmanci a jaddada cewa Daraktan yada labarai a ma’aikatar ba ya magana ga shugaban kasa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




