Labarai
Allah Ya Yi Zuri’a Rasuwa Lokaci Daya Cikin Daren Jiya Sanadin Hadarin Mota (Hotuna)


Advertisment
A cikin daren jiya Allah madaukakin sarki ya yi wa Nuhu Hamman Gabdo rasuwa tareda matarsa, ya’yansa hudu, da kuma diyar yayansa Hon. Babangida Nguroje tsohon maitaimakon Speaker na kasa dake zama a gidansa a sanadin mummunan hadarin mota daya faru da su cikin daren jiya.
Motar da tayi karo da wata ne lamarin da yasa nan take ta kama wuta, kuma dukkansu sun kone.
Ubangiji Allah ya jikansu da da rahama.
Tushen labari : Nasara