Labarai

Ana hana Hausa/Fulani ganin Likiti a asibitin jami’ar Jos saboda sunce su yan jihar Plateau ne

Advertisment

Idan Hausa/Fulani Musulmai suka rubuta su yan asalin Plateau ne a Fam, sai ace musu su canza saboda babu Hausa/Fulani a tarihin jihar.
Mutane sun dade suna korafin wannan batun dake gudana a asibitin JUTH gabanin bayyanar bidiyo dake nuna wata ma’aikaciyar asibitin tana tabbatar da hakan.kamar yadda Daily news hausa ta ruwaito
Asibitin JUTH dai ta gwamnatin tarayya ce ba ta jihar ba.
Daily Trust ta ruwaito cewa ta samu ji daga bakin wasu marasa lafiya da suka fuskanci wannan lamari yayinda suka je rijista cikin asibitin.
Idan mutum yaje rijista, ana bashi fam ya cika inda zai rubuta sunansa, kabilarsa, jiharsa na asali da karamar hukumarsa.
Amma idan Hausa/Fulani Musulmai suka rubuta su yan asalin Plateau ne, sai ace musu su canza saboda babu Hausa/Fulani a tarihin jihar.
Idan mutum yaki bin yadda sukace, ba zai ga Likita ba.
Saboda haka muna kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya tare da gwamnatin jihar Plateau da su shiga cikin wannan al’amarin domin bama ma’abota hakki hakkin su.
Domin irin wannan shike haifar da rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Dalili ko anan shine al’ummar jihar kano- katsina- Gombe – Bauchi – Zamfara – Kebbi – Jigawa – Sokoto da sauran jihohin arewa wanda Hausa/Fulani suka zamo mafiya rijaye suma sudau irin wannan tsarin na al’ummar jihar Plateau kuna ganin za’ai zauna lafiya kuwa?
Maganar Gaskiya itace baza’a zauna lafiya ba saboda haka maganin ayi kar’a fara.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button