Shugaba kasa Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar EFCC
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Ngelale ya bayyana cewa naɗin Olukoyede, na tsawon shekara hudu ne a matakin farko, amma sai majalisar dattawa ta tabbatar da shi.
Jaridar BBC Hausa na ruwaito sanarwar ta ce shugabancin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na ƙasar na samun sauye-sauye cikin ‘yan watannin da suka gabata, tun bayan hawan Bola Tinubu karagar mulki a ranar 29 ga Mayu.
A ranar 14 ga watan Yunin 2023, Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC, kuma har yanzu yana tsare a hannun hukumomi ba tare da an gurfanar da shi gaban shari’a ba.
Sanarwar ta ce Tinubu ya dakatar da Bawa ne “don ba da damar yin ingantaccen bincike kan yadda ya gudanar da aiki lokacin shugabancinsa”.
Matakin ya zo ne bayan zarge-zarge ”masu nauyi” na tozarta mukaminsa, in ji sanarwar.
Daga nan ne shugaban ya umurci daraktan ayyuka na hukumar Abdulkarim Chukkol ya rike shugabanci EFCC a mataki na wucin gadi.
Ngelale ya ce matakin da shugaban kasar ya dauka na nada Olukoyede a matsayin sabon shugaban EFCC ya samo asali ne daga damar da aka ba shi bisa tanadin dokar da ta kafa hukumar EFCC ta 2004, sashe na 2 karamin sashe na 3.
“Ola Olukoyede lauya ne mai gogewa tsawon shekaru sama da 22 a matsayin mai ba da shawara kuma kwararre ne kan gano laifukan damfara da kuma ƙididdige muhimman bayanai don masu mulki.” in ji Ngelale.