Labarai

Ba Abin da marigayiya Rabi’atu S. Haruna ta fi so kamar yabon Annabi, inji mijin ta

MIJIN fitacciyar mawaƙiyar Manzon Allah (s.a.w.), marigayiya Rabi’atu S. Harun, ya bayyana cewa ba abin da matar tasa ta fi so ta riƙa yi kamar yabon Manzon Allah.
Alhaji Shariff Mu’azu, wanda shi ma sha’iri ne, ya faɗa wa mujallar Fim cewa hakan ne ma ya sanya ba ta ce masa ta na so ta yi aikin albashi ba duk da yake ta na da ilimin addini da na boko.
Rabi’atu ta rasu ne da misalin ƙarfe 3:30 na yamma a gidan mijin ta da ke layin Ɗangaladima a Titin Abuja, unguwar Rigasa, Kaduna, a yau Talata, 16 ga Maris, 2021.
Shekarun ta 35 a duniya.
An yi jana’izar ta aka kai ta gidan ta na gaskiya a maƙabartar unguwar Hayin Ɗanmani.
Ita ce ta rera fitattun waƙoƙin nan masu taken ‘Sayyadin Nasi Karimi’ da ‘Mai Daraja Annabi Ma’aiki Gata Na’ waɗanda su ka yi tashe a shekarun baya.
An taru za a yi wa Rabi’atu S. Harun sallah
Mijin ta, Alhaji Shariff Mu’azu, ya shaida wa mujallar Fim cewa marigayiyar ta yi rashin lafiya na tsawon mako biyu, amma ta samu sauƙi kafin ciwon ya dawo.
Sayyada Rabi’atu ta rasu ta bar mijin ta da ‘ya’ya biyu, Ahmad da Khausar.
Da wakilin mujallar Fim ya tambayi mijin abin da zai iya cewa game da wannan babban rashi da ya yi, sai ya ce, “Gaskiya na yi rashi. Domin ta na da kirki, kuma ta na yabon Manzon Allah, don ba ta da wani buri a rayuwar ta da ya wuce wannan yabon, kuma da ya ke ni ma layi na ne sai na bar ta ta ci-gaba da yi.
“Ka ga kuma ta yi karatun boko daidai gwargwado, sannan ta yi karatun addini, don har Larabci ma ta na ji, amma ba ta taɓa nuna min ko za ta yi wani kasuwanci ko wani aikin gwamnati haka ba, sai dai yabon Annabi S.A.W. kawai, shi ya sa ni kuma na ƙarfafa mata gwiwa na ba ta dama ta ci gaba.
An kawo Rabi’atu S. Harun bakin kabarin ta
“Ni yanzu babu abin da zan ce sai dai fatan Allah ya jiƙan ta da rahama. Allah ya sada ta da Annabin Muhammadu s.a.w.”
Allahu Akbar! Da ma Allah ya ce dukkan mai rai sai ya ɗanɗani mutuwa.
Labarin mutuwar Rabi’atu ya girgiza farfajiyar mawaƙan begen Annabi Muhammad (SAW) da ma sauran jama’a. Labarin ya yaɗu a soshiyal midiya jim kaɗan da rasuwar, kuma duk wanda ya karanta labarin sai ya kaɗu kuma ya yi mata addu’a.
Mu ma a mujallar Fim mu na addu’ar Allah ya jiƙan Rabi’atu S. Harun da rahama, ya kuma albarkaci dukkan abin da ta bari, amin.
Ana rufe Rabi’atu S. Haruna
Allahu Akbar! Wannan ita ce kushewar masoyiyar Manzon Allah, Rabi’atu S. Harun, jim kaɗan bayan an rufe ta

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button