Yakamata kasashen Afrika sun fito a dama dasu akan yakin Ukraine kar su yamo yan baruwana
Jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce bai kamata ƙasashen Afrika su zama ƴan ba-ruwanmu a yaƙin Ukraine ba.
A yayin wata hira da BBC, Linda Thomas-Greenfield, ta bayyana cewa a ƙuri’ar da aka yi a babban zauren majalisar makonni biyu da suka gabata kan ƙin amincewa da kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine, ta ce ƙasashe 17 sun ƙi ɗaukar ɓangaren sai kuma ƙasashe takwas sun ƙaurace wa jefa ƙuri’ar baki ɗaya.
Jakadiyar ta ce babu batun zama ƴan ba-ruwanmu a wannan lamari kuma wannan yaƙin ba yaƙin caccar baka bane tsakanin ƙasashen Yamma da Rasha.
Ms Greenfield ɗin kuma ta ce kasarta za ta mara baya ga kudurin Afirka Ta Kudu na shiga tsakani a yakin na Ukraine.
Dakarun Rasha sun kasa matsawa ko’ina zuwa birnin Kyiv – Amurka
Dakarun Rasha “sun kasa yin gaba” a Ukraine, amma har yanzu suna da ƙarfin dakaru na kusan kashi 90 cikin 100, a cewar wani babban jami’in sojan Amurka.
Cikin wata sanarwa, jami’in ya ce dakarun Rasha “ba su samu wani ci gaba ba” zuwa birnin Kyiv, kuma “babu wani motsi da sojojin suka yi” zuwa gabashin birnin.
Sun ce jajircewar dakarun Ukraine ne dalili amma har yanzu birnin Mariupol da aka yi wa zobe yana nan yadda yake.
“Muna ci gaba da ganin luguden wuta a can tun bayan fara yaƙin,” in ji jami’in.
A cewarsa, Rasha ta harba makamai masu linzami fiye da 1,080 tun daga farkon yaƙin.
Sanarwar ta ce rahoton harin da aka ce an kai kusa da filin jirgin sama na birnin Lyviv da ƙanshin gaskiya a cikinsa, amma babu tabbas kan irin ɓarnar da ya yi zuwa yanzu.


