Labarai
Innalillahi wa’inna ilaihirraj’un : Allah Yayiwa Sarkin Zazzau Rasuwa
Advertisment
Allah Ya Yiwa Mai Martaba Sarkin Zazzau Hrh Alhaji Shehu Idris Rasuwa Yanzun Nan
Muna Adduar Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa.
Yanzun nan Allah Ya karbi rayuwar babban basaraken jihar Kaduna Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris yana da shekaru 84 da haihuwa
Sarkin ya shekara 45 yana sarautar Masarautar Zazzau a fadarsa dake garin Zaria, garin marigayi Malam Albaniy, ya koma ga Mahaliccin mu a yau Lahadi 20-9-2020
Yaa Allah Ka yafe masa laifukansa, Ka sa Aljannah ta zamto makoma a gareshi
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com