Labarai

Hukumar Kwastam a jihar Kebbi ta kama Trela makare da naman jaki na akallan N42M

Advertisment

Yayinda rundunar Hana fasakwabri reshen jihar Kebbi ta yi nassarar cafke wata babbar mota makil da naman jaki na dubban miliyoyi akan hanyar fita kamar yadda Rariya hausa na ruwaito a shafin Facebook
Ranar Asabar 5 ga watan Maris ne, jami’an hukumar ta reshen Birnin kebbi sun kama motar tirelar mai lamba ARG 323 XA makil da naman jaki wanda aka zankada su cikin buhuna.Hukumar Kwastam a jihar Kebbi ta kama Trela makare da naman jaki na akallan N42M
Kakakin hukumar Kuma shugaba na reshen jihar Kebbi Nasiru Manga, ya sanar wa manema labarai a wata takarda da ya fitar amadadin Konturola na hukumar reshen jihar Kebbi. Ya ce duk da yake an biya kudin kaidar watau Duty na Naira miliyan 42,534,400.
Sai dai ya ce kasuwancin haramtacce ne bisa dokar kasa ta Section 63 (b) of CEMA CAP C.45 LFN 2004, wanda ya jibanci harkar naman jaki da saurar dokoki.
Daga karshe rundunar ta kone naman jakin, a gaban wakilan hukumomin DSS, NESREA, da kuma yansanda.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button