Uncategorized

Ku Zabi Bola Ahmed Tinubu Ina Da Yakinin Ba Zaku Yi Da Na Sani Ba – In Ji Sa’adatu Dogon Bauchi

Shugabar Kungiyar ata Masu Rajin Goyon Bayan Takarar Sanata Bola Ahmed Tinubu A Arewacin Najeriya Hajiya Sa’adatu Garba Dogon Bauchi, ta bukaci mata a Jihar Katsina akan su marawa dan takarar baya domin cimma nasara a zaben 2023 kamar yadda Jakadiyar RTV
Shugabar Matan ta yi wannan kiran ne a sa’ilinda take zantawa da manema labarai a Katsina.Ku Zabi Bola Ahmed Tinubu Ina Da Yakinin Ba Zaku Yi Da Na Sani Ba – In Ji Sa’adatu Dogon Bauchi
Kamar yadda ta bayyana, dan takarar nasu Sanata Bola Ahmed Tinubu, yana da karfin gwuiwar daukar yan Najeriya ya kaisu gachi, lura da kwarewarshi a harkokin shugabanci da mu’amala da mutane da yake yi a kowane bangare na kasar nan.

Hajiya Sa’adatu Dogon Bauchi ta tabbatar da cewar yan Najeriya ba zasu yi nadamar zaben Sanata Bola Ahmed Tinubu ba muddin suka bashi dama na ya Shugabanci kasar.
Tayi magana mai tsawo akan tsare-tsare da Sanata Bola Ahmed Tinubu ya shirya domin kyautata rayuwar yan kasarnan idan ya zama Shugaban Kasa.
Shirye-shiryen sun hada da samar da ababen yi ga mata da matasa, tallafawa masu karamin karfi da inganta tsaro da kiwon lafiya gami da inganta harkokin noma da ilimi da dai sauransu.

Daga nan sai ta yi albishir ga matan Jihar Katsina cewar akwai tsare-tsare da dama da Sanata Bola Ahmed Tinubu ya shirya da suka shafi rayuwar mata kai tsaye domin su san cewa an kula da su.

Hajiya Sa’adatu Dogon Bauchi ta kuma karyata wasu maganganun batanci da wasu marasa kishi suke yi akan dan takarar na su wanda ta bayyana a matsayin adawa ta makanta da son zuciya.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button