Labarai
Yanzu – Yanzu : KotuTa Dakatar Da Sabon Sarkin Zazzau Amb Ahmad Nuhu Bamalli (Hotuna)
Advertisment
Wata sabuwa inji yan chacha yanzu Majiyarmu ta samu daga wani shugaban masu sauraren murya talaka zainadu bala kofar sabuwa da wallafa wani labari mai ban mamaki da al’ajabi.
Ga jawabin da ya wallafa a shafinsa na facebook.
“Wata babbar kotu a jihar Kaduna karkashin jagoranci mai shari’a K Dabo ta dakatar da sabon sarkin Zazzau Amb. Ahmad Nuhu Bamalli daga amsa sunan sarkin Zazzau, har sai ta zauna ta saurari shari’ar da Iyan Zazzau Bashir Aminu ya shigar a gabanta.
Tun a kwanakin baya ne dai Iyan Zazzau ya maka sabon sarkin Zazzau da gwamnatin jihar Kaduna a gaban kotu inda yake kalubalantar hanyar da Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya zama sarkin Zazzau.”
Ga Hotuna nan kasa ku kalla.