[Bidiyo] bidiyon da Dr Abdallah G/kaya ke bayyani akan zargin ma’aikatan lafiya da aikata zina


Malamin addinin Musulunci Sheikh Abdallah Usman Godon Kaya ya janye ikirarin da ya yi kan ma’aikatan lafiya na Najeriya cewa wasunsu na aikata masha’a yayin da suke aikin dare a asibitocin kasar.
Cikin wani jawabi da ya yi da aka gani a wani bidiyo, malamin addinin Musuluncin ya zargi ma’aikatan lafiyan da mu’amular da ba ta dace ba, ciki har da zina da cin zarafin mata.
Tun da farko jaridar intanet ta Sahelian Times ta ruwaito shehin malamin yana zargin ma’aikatan lafiya da aikata zina yayin wani shirin talabijin da aka haska a tashar talabijin ta Africa TV mai zaman kanta.
Sai dai daga baya ta ce baya malamin ya janye kalaman nasa, bayan da ƙungiyar ma’aikatan jinyan ta ce kalaman nasa ɓata wa ƴaƴanta suna ne, tare da neman ya janye su.
Ga bidiyo nan kasa.
Wannan shine bidiyon da malam yake karfafawa da nuna muhimmancin sanya yayanmu cikin karatun harka lafiya wanda har malam yake cewa yanzu yarsa ta kamala midwifery dan kuma tana karatun medicine.
