Osinbajo Ya Rattaba Hannu Kan Muhimman Dokoki Ukku
OSINBAJO YA RATTABA HANNU KAN MUHIMMAN DOKOKI UKU
Mukaddashin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya rattaba hannu kan wasu dokoki uku wadanda fadar shugaban kasar ta ce za su kawo gagarumar sauyi game da yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati a Nigeria.
Wata sanarwar da mai magana da yawun Farfesa Osinbajo, Laolu Akande, ya fitar, ta ce daya daga cikin sabbin dokokin, za ta sa ma’aikatun gwamnati su fi bayar da fifiko kan hulda da kamfanoni da kuma ‘yan kwangila na cikin gida kan cinikayyar gwamnati.
An kuma sa hannu a dokar da zata saukaka yanayin kasuwanci ga kamfanoni da ‘yan kasuwa masu zuba jari ko fitar da amfanin gona daga Najeriya da kuma saukaka shige da fice daga kasar.
Doka ta ukun da Farfesa Osinbajo ya rattaba wa hannu tana neman tilasta wa ma’aikatun gwamnati gaggauta mika bayanan kasafin kudi na shekara uku ga ministan kudi da na kasafin kudi da tsare-tsare a karshen watan Yuli.
Sanarwar ta ce kafin ya rattaba hannu kan dokokin, Farfesa Osinbajo ya gana da ministoci da shugabannin ma’akatun gwamnatin da dokokin suka shafa a fadar gwamnatin kasar.
Sakkwato Birnin Shehu
19th May, 2017