Muaz Magaji win win ‘ya kurumce’ yayin da kotu ta umurci ‘yan sanda su kai shi asibiti


An cafke Magaji ne bayan da garin gujewa kamu ya ci karo da fitilar kan titi a motarsa.

Da yake baiyana gaban Alkalin Kotun, Aminu Gabari a yau Juma’a, Lauyan Magaji, Gazzali Ahmad, ya ce wanda yake karewa ya rasa ji na ɗan wani lokaci sakamakon raunin da ya samu bayan fitar da jakar iska ta yi a motarsa.
Ahmad ya ƙara da cewa wanda ake tuhumar ba zai iya sauraron tuhume-tuhumen da ake masa balle ya amsa ko akasin haka.
Don haka lauyan ya roƙi kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa domin nemar masa lafiya a asibiti.

Da yake yanke hukunci kan buƙatar lauyan, Gabari ya ba da umarnin a kai Magaji asibitin shalkwatar ‘yan sanda kuma ya ci gaba da zama a hannun ‘yan sanda.
Sai Gabari ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Litinin, 31 ga watan Janairu.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




