Kannywood
Yakamata gwamnatin najeriya ta rufe tik tok – sarkin waka Nazir M Ahmad
Advertisment


Sarkin Waƙa ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar .
“Ya kamata gwamnati ta dakatar da TikTok a Najeriya tun kafin lokaci ya ƙure”, in ji shi.
A iya jiya da daddare kimanin mutane 657 ne suka bayyana ra’ayinsu a ƙarƙashin wannan wallafa da Sarkin Waƙa ya yi, inda wasu suke goyon bayan sa wasu kuma suke sukar sa.
Mutane da dama dai a Najeriya suna da ra’ayin mahukunta su toshe manhajar TikTok sakamakon yadda wasu ‘yan mata ke amfani da ita ba ta yadda ya dace ba.



