Tsohon limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-finai
Tsohon limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani, ya bayyana a wani gajeriyar tallar wani fim mai suna Combat Zone
Bayan wallafa bidiyon a Twitter, Sheikh Al-Kalbani ya je kasa inda yayi tsokacin cewa, kuna ganin zan iya kasuwa a Hollywoood?
Wannan al’amarin ya tashi hankalin jama’a inda aka dinga masa tsokaci tare da fatan samun shiriyar Allah gare shi
A wani bidiyo mai tsawon minti biyu da dakika arrba’in da daya, tsohon limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya bayar da cikakken gabatarwa na matsayinsa.


Kamar yadda The Islamic Information da Legit suka ruwaito, Fim din mai suna Combat Zone, ya shahar tunda tsohon limamin Kaaba Imam Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani da wasu ‘yan kwallon kafa ne suke tallarsa
Sheikh Adil Al-Kalbani ya bayyana a wani bidiyo na talla wanda ke bayyana sojoji suna yaki kuma suna amfani da makamai. A cikin gajeren bidiyon, an ga limamin Ka’aban ya na bayani dalla-dalla.
Hukumar kula da nishadi ta kasar Saudi Arabia ce ta wallafa bidiyon a shafin Turki al-Sheikh na Twitter.
A kasan wannan wallafar, tsohon limamin Ka’aban, Sheikh Adil Al-Kalbani ya je cike da ba a inda ya wallafa, “Kuna tunanin zan iya zuwa masana’antar fina-finai ta turawa?” a kasan bidiyon da aka wallafa.
Ma’abota amfani da kafafen sada zumunta sun caccaki Sheikh Al-Kalbani bayan ya bayyana a bidiyon.
Wani ya ce a gaskiya ganin shi a bidiyon ya zama banbarakwai, wani kuma martani yayi da cewa, “Allah ya shiryar da kai kuma ya bude maka zuciya.”
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





