Uba Sani ya maido wa Musulman Unguwan Dosa filin Idin da gwamnatin El-Rufai ya yanka aka raba don gina gidaje
Wasu daga cikin malaman dake da’awa na addinin musulunci a jihar Kaduna sun bayyana godiyar su ga gwamnan Kaduna, Uba Sani, bisa dawo musu da filin masallacin Idi dungurungun ɗin sa da ya yi wa al’ummar unguwan.
Jaridar premium Times Hausa na ruwaito limamin Masallaci Lere Street dake Kaduna, ya samar wa Al’umman unguwar cewa gwamna Sani ya sanar wa al’ummar unguwar cewa gwamnati ta dawo wa al’ummar unguwar wannan fili domin ci gaba da Sallar Idi kamar yadda aka saba.
Ya ce ” Dukkan malamai musamman na unguwar za su halarci wannan fili domin sake duba shi sannan kuma ayi hotunan murna da wannan albishir.
” A baya gwamnatin baya ta yakice wani sashe na filin in da muka ji kishin kishin ɗin za a raba su ne domin a gina gidaje, amma yanzu wannan gwamnati ta daeo mana da filin dukkan sa.