Labarai

Tsohon limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-finai

Tsohon limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani, ya bayyana a wani gajeriyar tallar wani fim mai suna Combat Zone
Bayan wallafa bidiyon a Twitter, Sheikh Al-Kalbani ya je kasa inda yayi tsokacin cewa, kuna ganin zan iya kasuwa a Hollywoood?
Wannan al’amarin ya tashi hankalin jama’a inda aka dinga masa tsokaci tare da fatan samun shiriyar Allah gare shi
A wani bidiyo mai tsawon minti biyu da dakika arrba’in da daya, tsohon limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya bayar da cikakken gabatarwa na matsayinsa.

Tsohon limamin Ka'aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-finai
Tsohon limamin Ka’aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-finai

Kamar yadda The Islamic Information da Legit suka ruwaito, Fim din mai suna Combat Zone, ya shahar tunda tsohon limamin Kaaba Imam Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani da wasu ‘yan kwallon kafa ne suke tallarsa
Sheikh Adil Al-Kalbani ya bayyana a wani bidiyo na talla wanda ke bayyana sojoji suna yaki kuma suna amfani da makamai. A cikin gajeren bidiyon, an ga limamin Ka’aban ya na bayani dalla-dalla.

Hukumar kula da nishadi ta kasar Saudi Arabia ce ta wallafa bidiyon a shafin Turki al-Sheikh na Twitter.
A kasan wannan wallafar, tsohon limamin Ka’aban, Sheikh Adil Al-Kalbani ya je cike da ba a inda ya wallafa, “Kuna tunanin zan iya zuwa masana’antar fina-finai ta turawa?” a kasan bidiyon da aka wallafa.
Ma’abota amfani da kafafen sada zumunta sun caccaki Sheikh Al-Kalbani bayan ya bayyana a bidiyon.

Wani ya ce a gaskiya ganin shi a bidiyon ya zama banbarakwai, wani kuma martani yayi da cewa, “Allah ya shiryar da kai kuma ya bude maka zuciya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA