Labarai
Mun dade ba mu ji duriyar Kim Jong-Un ba – Amurka
Advertisment
Sakataren harkokin Amurka, Mike Pompeo ya ce jami’an Amurka sun ce ba su ga shugaban Koriya ta Arewa ba a ‘yan kwanakin nan, Kim Jong-un kuma suna sa ido kan rahotannin lafiyarsa.
Ya kuma bayyana damuwarsa dangane da hasashen da suke da shi na barkewar annobar korona ko kuma yunwa.
Mista Kim mai shekara 36 dai ba a kara ganin sa a bainar jama’a ba tun ranar 12 ga watan Afrilu lokacin da ya bayyana a gidan talbijin din kasar.
To sai dai jami’an gwamnatin Koriya ta Kudu sun ce rahotannin ba gaskiya ba ne.
Rashin bayyanar Kim Jong-un a wasu tarukka da ya saba halarta ne dai ya janyo rade-radin ko shugaban na Koriya ta Arewa na raye cikin koshin lafiya.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com




