Albishir Ga Talakawan Najeriya: Muhimman Abubuwan Aka Tauna a Taron Shugaban Kasa da Gwamnonin Jihohi
A jiya ne shugaban kasa Bola Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima suka gana da gwamnonin jihohi 36 da wasu ministoci da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnatin tarayya.
Taron dai ya yi nasarar amincewa da matsaya guda don tinkarar wasu kalubalen da kasar ke fuskanta a halin yanzu musamman tsadar abinci da rashin tsaro.
Bayan tattaunawa mai zurfi shugaban kasa da gwamnonin sun amince da yin aiki tare don magance matsalolin tsaron da na tattalin arziki da ‘yan kasar ke fuskanta.
Ga mahimman abubuwan da shugaban ya gaya wa Gwamnonin su yi:
1. A kan magance matsalar rashin tsaro wanda kuma ke shafar noma da samar da abinci, shugaba Tinubu ya bayar da umarni guda 3.
👉🏽Daukar karin jami’an ‘yan sanda domin karfafa rundunar tsaro
👉🏽Hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi da ma Majalisar Dokoki ta kasa don samar da taswirar kafa ‘yan sandan Jihohi maimakon ‘yan banga da ake amfani da su a wasu Jihohin a yanzu
👉🏽 Shugaban ya bukaci Gwamnonin da su karfafa mafarauta tare da ba su makamai domin kare dukkan dazuzzuka daga masu aikata laifuka.
👉🏽Yadda za a shigar da samar da ‘yan sandan Jiha cikin tattaunawa a Majalisar Tattalin Arzikin Kasa.
2. Akan tsadar kayan abinci kuwa, Shugaban ya ba da umarnin cewa gwamnatocin Jihohi da gwamnatin tarayya su hada karfi da karfe don kara samar da abinci a cikin gida.
Shugaban ya ba da shawarar a hana shigo da abinci da kuma tsayar da farashi na bai daya a lokacin da ya kamata sannan a karfafa giwar masu samar da abinci na cikin gida don habaka samar da abincin.
3. Shugaban ya shawarci Gwamnoni da su yi koyi da jihar Kano wajen tunkarar masu boye kayan abinci don cin kazamar riba da ‘yan kasuwar ke yi.
Shugaban ya umurci Sufeto-Janar na ’yan sanda, da mai ba da shawara kan harkokin tsaro, da na ma’aikatar harkokin gwamnati, da su sanya ido a kan rumbun adana kayayyakin abinci a fadin kasar nan, tare da tsaigaita cin kazamar ribar ‘yan kasuwa.
4. Shugaban ya bukaci gwamnonin da su mai da hankali wajen bunkasa kiwon dabbobi a jihohinsu da kuma kara yawan kiwon kaji da kamun kifi.
5. Shugaban ya roki Gwamnonin da su tabbatar da cewa an biya duk wani bashin albashin ma’aikata, da kudaden ‘yan fansho da garatuti a matsayin hanyar sanya kudi a hannayen jama’a tunda yanzu jihohi suna samun karin kudaden shiga na FAAC duk wata.
“Don Allah Ku kashe kudin, kada ku kashe mutanen” in ji shugaban.
6. Shugaba Tinubu ya roki Gwamnoni da su kara samar da guraben ayyukan yi ga matasa a jihohinsu domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Fassarar rubutun Bayo Onenuga, daga Rahma Abdulmajid.