Labarai

Ba Sai An Sha Magani Ba Ake Warkewa Daga Cutar Corona Virus Ba – NCDC

Advertisment

Daga Comr Abba Sani Pantami

Shugaban NCDC, Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya, Dr Chikwe Ihekweazu, ya ce kaso 95 zuwa 98 na masu dauke da cutar korona a kasar za su warke garau.

Dr Chikwe ya ce kusan dukkanin wadanda cutar korona ta harba a kasar nan za su murmure ba tare shan wani magani ba ko samun kulawa ta kwararrun lafiya ba.

Advertisment

Furucin Dr Chikwe ya zo ne cikin birnin Abuja a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilun, yayin ganawa da kwamitin kar ta kwana da fadar shugaban kasa ta kafa a kan cutar korona.

A cewarsa, ba wani dalili ya sanya ake kebance masu cutar a killace ba face hana yaduwarta kadai. Amma cutar ba wata tsiya bace. A kalamansa: “Alamomin cutar korona ba su bayyana ba a jikin mafi akasarin wadanda ta harba kuma za su murmure ba da dade wa ba.

Dalilin kadai da ya sanya muke kebance wadanda cutar ta harba a cibiyoyyin killacewa bai wuce fafutikar mu ta hana yaduwarta ba gwargwadon iko.

Sai dai ya ce “kashi 5 zuwa 15 cikin 100 bisa la’akari da inda suke, za su kuma da tsananin rashin lafiya ta cutar kuma wasun su za su mace.

A halin yanzu akwai jihohi 36 da cutar ta bulla ciki har da babban birnin kasar nan, sai dai shugaban na NCDC ya yi gargadin cewa babu jihar da ta tsira daga hadarin barkewar cutar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button